Kiwon Lafiya
Saura shekaru 27 Bayin Allah su daina mutuwa idan har sun ga dama. Mutuwa za ta zama sai wanda ya ke so ya bar Duniya kamar yadda José Cordeiro da kuma David Wood su ka bayyana kwanan nan.
Tsawon shekaru aru-aru 'baure wani nau'in dangin kayan marmari ne da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Wani bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka.
Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai.
Cibiyar lafiya WHO cikin wata sabuwar matashiyar jagora da ta fitar dangane da yadda ya dace a yi ta'ammali da sukari a kowace rana, ta ce domin neman zama cikin koshin lafiya kada mutum ya sha sukari da ya haura ma'aunin gram 25.
Idan aka ce Hepatitis, toh ana nufin ciwon Hanta kenan a Hausance. Hepatitis kasu iri daban-daban har guda biyar, inda suka hada da; Hepatitis A, Hepatitis B, Hepatitis C, Hepatitis D, Hepatitis E.
A yau ne ranar ciwon hanta ta duniya wato World Hepatitis Day. Allurar riga kafin ciwon hanta wasu allurori ne guda uku zuwa hudu da ake yi na tsawon watanni 6. Ba'a kamuwa da ciwon hanta matukar an yiwa mutum alluran riga kafi.
Alamomin cutar hanta sun rabu kashi daban-daban daga kanana zuwa manya. Su kan bayyana a jikin dan Adam bayan wata daya zuwa watanni hudu da kamuwa da cutar. A wani sa'ilin su kan bayyana bayan mako biyu da kamuwa.
Babu shakka masana sun yi itifakin cewa rashin gamsuwa a wurin saduwar iyali a tsakanin ma'aurata na daya daga cikin manyan dalilai dake haddasa matsaloli da a wani sa'ilin take janyo mutuwar aure.
Masana sun bukaci jama’a da su dunga yawan cin gwaza domin cewa yana dauke da sinadarai masu matukar amfani a jikin dan adam. Bincike ya kuma nuna cewa ganyen gwaza na dauke da sinadarin kawar da cututtuka da suka hada da makanta.
Kiwon Lafiya
Samu kari