Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

Fadar shugaban kasar Najeriya ta fara gudanar da tantance ma’aikata da kuma bakin dake ziyartar fadar dake babban birnin tarayya Abuja biyo bayan samun bullar annobar cutar Coronavirus mai suna COVID-19 a Najeriya a ranar juma’ar da ta gabata.0

Jaridar Daily Trust ta bayyana an tura jami’an kiwon lafiya a kofar karshe ta shiga ofisoshin dake cikin fadar shugaban kasa don su tabbatar ma’aikatan fadar gwamnatin tare da baki masu kai ziyara sun wanke hannayensu da ruwan wanke hannu na musamman domin kashe kwayoyin cututtuka dake hannuwan.

KU KARANTA: Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta

Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus
Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus
Asali: Twitter

Haka zalika jami’an kiwon lafiyan suna amfani da na’urar gwada zafin jikin mutum domin gwajin yanayin zafin ma’aikatan Villa da kuma baki, daga cikin wadanda aka yi ma wannan gwaji a ranar Talata akwai ministan kwadago, Chris Ngige wanda ya isa fadar da misalin larfe 4:50 na rana.

Bugu da kari majiyar Legit.ng ta ruwaito an samar da ruwan wankin hannun na musamman da na’urar gwajin yanayin zafin jikin dan adam a sakatariyar kungiyar gwamnonin Najeriya dake Abuja tun a ranar Juma’ar da aka fara samun bullar cutar a Najeriya.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa tare da cibiyar kare yaduwar cututtuka sun samar da cibiyar daukan matakan gaggawa domin magance yaduwar cutar a Najeriya.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bara game da zargin da ake yi masa da hannu cikin badakalar kudin makamai a zamanin da yake minista, sa’annan ya wanke manyan hadimansa guda biyu, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje.

A makon nan ne wasu rahotanni daga jaridu daban daban suka bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kaddamar da bincike a kan badakalar kwangilar sayo makamai da aka yi a ma’aikatar tsaro a shekarar 2008.

Sai dai Kwankwaso ya kasance ministan tsaro ne daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2006, kamar yadda tsohon gwamnan ya tabbatar da kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: