Yadda Karnuka Suka Farmaki Tsohuwar Sojar Amurka Suka Kashe Ta
- Wata tsohuwar sojar rundunar sojin Amurka mai shekaru 36, Allison Lynn Anderson, ta rasu bayan wasu karnuka sun far mata a jihar Georgia
- Allison, wacce uwa ce ga yara uku, an same ta da munanan raunukan da suka yi sanadin mutuwarta a ranar 16 ga Nuwamba
- Yarinyarta ta bayyana alhini kan mutuwar mahaifiyarta, tana mai cewa ta rasa damar sanar da ita cewa za ta zama kaka a karon farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Wata tsohuwar sojar rundunar sojin Amurka, Allison Lynn Anderson, mai shekaru 36, ta mutu bayan wasu karnuka sun far mata a garin Cartersville da ke jihar Georgia, Amurka.
An gano gawar Anderson dauke da munanan raunuka a ranar 16 ga Nuwamba, bayan ’yan sanda sun samu rahoton wata mata da ba ta motsi a kusa da wani gini da aka bari babu kowa.

Source: Facebook
Daily Mail ta rahoto cewa hukumar binciken manyan laifuffuka ta jihar Georgia ta bayyana cewa binciken farko na gawar ya nuna yadda karnukan suka kai mata hari, amma ba ta bayyana adadin karnukan da suka yi hakan ba.
An kama wasu daga cikin karnukan
Rahotanni sun nuna cewa jami’an kula da dabbobi na karamar hukumar Bartow sun kama wasu daga cikin karnukan da ake zargin sun kai wa Anderson hari.
A halin yanzu, masu bincike na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, ciki har da nazarin hotunan na’urorin daukar bidiyo na tsaro da ke yankin.
’Yar tsohuwar sojar ta yi alhini
Rahoton da NBC ta wallafa ya nuna cewa Anderson ta shiga rundunar sojin Amurka a shekarar 2007, kuma ta bar ’ya’ya uku a duniya.
Abin takaici, ta rasu ba tare da sanin cewa ’yarta mai shekaru 20, Miley Garner, na dauke da cikin jikanta na farko ba.
Garner, wacce ke jiran haihuwa tare da saurayinta Jesse Jarrett, ta ce mahaifiyarta za ta yi matukar farin ciki da jin labarin cikin.
Ta ce:
“Da mahaifiyata ta san cewa ina dauke da cikin jikanta na farko, da ta yi matukar farin ciki da murna.”
Ta kuma bayyana takaicinta kan yadda masu karnukan suka kasa kula da su, tana mai cewa abin da mahaifiyarta ta sha azaba ne.

Source: Facebook
Garner ta ce mahaifiyarta ta cancanci a yi mata adalci, duk da cewa tana ganin za ta iya yafewa wadanda ke da alhakin faruwar lamarin.
Amurka za ta koro 'yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Amurka ta kara sunayen ’yan Najeriya 24 cikin jerin mutanen da take shirin kora daga kasar, lamarin da ya kai adadin wadanda ke cikin jerin zuwa 157.
Ana zargin mutanen da aikata laifuffuka daban-daban da suka hada da damfara, safarar miyagun kwayoyi, satar bayanan sirri da halatta kudin haram.
Sai dai kasar ba ta bayyana lokacin da za a gudanar da korar ba, kuma sanya sunan mutum cikin jerin ba yana nufin kotu ta same shi da laifi ba.
Asali: Legit.ng

