Barau Jibrin Ya Hada Kan Malaman Musulunci 2,000 saboda Tinubu, Abba Kabir
- Sanata Barau Jibrin, ya nemi goyon bayan malaman addinin Musulunci sama da 2,000 daga Kano ta Arewa
- Barau Jibrin ya bayyana ayyukan raya ƙasa da gwamnatin tarayya ta kawo Kano, yana mai cewa Tinubu na da niyyar kawo ci gaba
- Barau ya kuma sanar da shirin rabon babura 390 da tallafin N50,000 ga kowane malami domin tallafa musu a ƙananan hukumomi 13
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya gana da malaman addinin Musulunci sama da 2,000 daga ƙananan hukumomi 13 na Kano ta Arewa.
Barau ya nemi su taimaka wajen wayar da kan jama’a domin samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da sauran ’yan takarar APC a zaɓen 2027.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, sanatan ya yaba wa malaman bisa addu’o’insu da gudummawar da suke bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano.
Manufar Tinubu ga yankin Arewa
Barau ya yi wannan kira ne a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da kyakkyawar manufa ga Kano, Arewa maso Yamma, yankin Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Ya bayyana malaman a matsayin iyaye da shugabanni, yana mai cewa addu’o’insu na daga cikin abubuwan da suka taimaka masa da sauran shugabanni wajen samun matsayinsu na yanzu.
Barau ya ce Kano na daga cikin manyan jihohin Afirka, kuma yana ganin addu’o’in malaman addini sun taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban jihar.
Ya kuma tuna da irin rawar da Kano ta taka a tarihin ci gaban Najeriya, musamman gudummawar marigayi Malam Aminu Kano da sauran fitattun ’yan asalin jihar.
Mataimakin shugaban majalisar ya ce bayan zaɓensa a shekarar 2023, ya zama mutum na farko daga Kano da ya taɓa riƙe muƙamin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

Source: Facebook
Martanin malamin Musulunci a Kano
A nasa jawabin, shugaban majalisar limaman Kano ta Arewa, kuma babban limamin ƙaramar hukumar Bichi, Malam Lawal Imam, ya yaba wa Barau bisa ayyukan da yake yi a Kano ta Arewa, ciki har da gina masallatai.
Ya ce malaman za su ci gaba da yi wa Barau, APC da Najeriya baki ɗaya addu’a, yana mai bayyana cewa malamai na da babban tasiri a cikin al’umma ta hanyar iyalansu, ɗalibansu da mabiyansu.
Ya ƙara da cewa:
“Za mu ci gaba da yi masa, APC da kuma ƙasar baki ɗaya addu’a. Malamai na da babbar hanyar isa ga jama’a. Kowannenmu yana da ’yan uwa, ɗalibai da mabiya da suke kallonmu a matsayin jagorori. Tasirinmu a cikin al’umma yana da yawa.”
Barau ya ce Tinubu ne da nasara
Mun ba ku labarin cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya ce duk alamu na nuna Shugaba Bola Tinubu zai lashe zaɓen 2027.
Barau ya yi wannan hasashen ne yayin ƙaddamar da kwamitocin yaƙin neman zaɓen APC a ƙananan hukumomi uku na Jihar Kano.
Ya buƙaci ’yan jam’iyyar APC su haɗa kai su yi aiki domin samun nasarar ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen mai zuwa.
Asali: Legit.ng

