Gwamnonin Arewa 19 Sun Yi Tarayya wajen Tsige Shugabannin Majalisar NDDC
- Gwamnonin Arewa sun dauki matakin korar shugabannin da ke rike da Majalisar da ke sa ido a kan ayyukan NDDC
- An ruguza kwamitin ne kamar yadda doka da tsari suka tanada domin a yi gyara a kamfanin da jihohi suka mallaka
- Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya yi bayanin hikimar sallamar shugabannin da dalilin neman kawo wasu sababbi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 sun rusa kwamitin gudanarwa na kamfanin NNDC wanda suka yi tarayya wajen mallaka.
Gwamnonin sun ruguza majalisar da ke sa ido kan harkokin NDDC, kuma suna shirin kafa sabon majalisa da za ta inganta ayyukan kamfanin.

Source: Facebook
Gwamnonin Arewa sun cin ma matsaya a taro
An cimma matsayar ne a ranar Talata, yayin wani taron musamman na masu hannun jari da aka gudanar a Kaduna a cewar jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Katsina ta ɗauki mataki kan Sarkin Daura bayan ɓullar bidiyonsa da baturiya
Sakatarorin gwamnatocin jihohin 19 ne suka halarci taron domin wakiltar gwamnatocinsu a matsayin masu hannun jari a cikin kamfanin na Arewa.
Sai dai, matakin korar shugabannin zai fara aiki ne bayan an amince da kudurorin da suka dace a babban taron kamfanin tare da bin dukkan ka'idoji.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron, Sakataren Gwamnatin Jihar Gombe, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, ya fadi hikimar hakan.
Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya ce masu hannun jarin sun amince da yin cikakken garambawul ga kamfanin domin sake fasalinsa da ayyukansa.
Hikimar waje da shugabannin majalisar NDDC
Ya ce manufar wannan mataki ita ce karfafa tsarin tafiyar da kamfanin, inganta shugabanci, tabbatar da cewa NDDC yana aiki yadda ya dace.
An kuma ci burin maida NNDC wata babbar cibiyar zuba jari da ci gaba da za ta amfani tattalin arzikin jihohi 19 da ake da su Arewacin kasar.

Kara karanta wannan
Gwamna ya fallasa yadda APC ke ɗauko hayar matasa su halarci yaƙin neman zaben Tinubu
Farfesan ya bayyana cewa za a kafa sabon kwamitin gudanarwa domin samar da jagoranci mai inganci da kuma sanya ido kan ayyukan kamfanin
Blueprint ta ce za a ba sabuwar majalisar alhakin tsara manufofin tafiyar da kamfanin da kyau.
Ya ce za a yi la'akari da hannun jarin kowace jiha, dokokin kamfanin da kuma tanade-tanaden dokar kamfanoni ta Najeriya ta 2020 wajen nadin.
Gwamnonin Arewa sun amince da wadanda za a nada
Rahoton ya ce ya kara da cewa masu hannun jarin za su amince da sunayen wadanda za a nada a matsayin sababbin daraktocin kamfanin bisa ka’ida.
A cewarsa, bayan kafa sabon kwamitin, za a umarce shi da ya gudanar da cikakken nazari kan tsarin gudanarwar kamfanin da kuma ma'aikatansa.
Za a yi duba ga tsarin gudanar da harkokin ofisoshi, ayyukan NDDC da kuma irin nasarorin da ya samu.
Za a binciki kudi da kadarorin kamfanin NDDC
Farfesa Njodi ya bayyana cewa sabon kwamitin zai gudanar da cikakken bincike kan harkokin kudi, gudanarwa, kadarori da tsarin shugabancin kamfanin.
Binciken zai maida hankali kan halin da kamfanin yake ciki ta fuskar kudi, kadarorinsa, basussukansa, jarin da ya zuba a wasu kamfanoni da kasuwancinsa.

Kara karanta wannan
Amurka ta kara sunayen 'yan Najeriya 24 cikin wasu 157 da za a fatattako daga kasar
Haka kuma, za a duba yadda jarin da kamfanin ya zuba ke samar da riba, ko yana bin dokokin kasa da ka'idojin gudanar da kamfanoni, da kuma yarjejeniyoyi.
Za a kuma duba irin rawar da tsohon kwamitin gudanarwa da shugabannin kamfanin suka taka, tare da gano ko sun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Source: Facebook
Alkali ya rike kudin gwamnoni a banki
Labarin nan ya ce kotu ta bayar da umarnin rike Dala miliyan 100 (kimanin naira biliyan 135.58) da aka ce Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta rike wa wani lauya.
Wannan matakin ya biyo bayan ƙarar da wani lauya, Ted Iseghohi-Edwards, ya shigar yana neman a biya shi ragowar kuɗin aikinsa na shari’a kan bashin Paris Club.
Alkali ya hana gwamnonin jihohi taɓa kuɗin da ke asusun NGF a banki har sai an kammala shari’ar da aka ɗage sauraron ta zuwa ranar 1 ga Disamba, 2026.
Asali: Legit.ng