Kiwon lafiya: Za mu iya rage yawan fitan da mutane su ke yi neman magani – Mamora

Kiwon lafiya: Za mu iya rage yawan fitan da mutane su ke yi neman magani – Mamora

Karamin Ministan harkar lafiya na Najeriya, Olorunnimbe Mamora, ya ce Najeriya ta na cikin wadanda ta ke amfana da zuwan mutanen kasar wajen ganin Likita.

Sanata Olorunnibe Mamora ya yi wannan bayani ne a Ranar Litinin a Garin Abuja, inda ya ce a da a kan zo Najeriya daga kasashen ketare domin samun saukin rashin lafiya.

Mai girma Ministan lafiya ya nuna cewa shekaru 50 zuwa 60 da su ka wuce, babban asibitin koyar da aikin Likitanci na Ibadan ya na cikin wadanda su ka yi fice a Duniya.

“A shekarun 1950s da 1960s, Najeriya ta kan jawo masu zuwa neman magani, har ‘Yan gidan sarautar kasar Saudiyya su kan zo asibitin Jami’ar Ibadan domin ganin Likita.”

“Wasu su kan je kasashen waje domin su samu na’urori da kayan aikin da babu a Najeriya. Dole mu dage mu ga cewa mun samu wadannan na’urori domin a daina balaguro”

KU KARANTA: Minista ya durkusa har kasa domin gaida shararriyyar 'Yar wasa

Kiwon lafiya: Ba za a iya hana mutane yawon neman magani ba – Mamora
Sanata Mamora ya ce da asibitocin Najeriya sun yi kaurin-suna
Asali: UGC

Mai girma Ministan ya ce gwamnatin tarayya za ta kara kokari wajen samar da isassun kayan aiki da kwararrun ma’aikata da na’urorin da aka rasa a asibitocin Najeriya.

“Aikin mu a matsayin kasa shi ne mu tanadi kayan asibiti domin kula da lafiyar ‘yan kasa. Da zarar an samu wannan, za a rage fita zuwa asibitocin da ke kasashen waje.”

A cewar Ministan, idan har Najeriya ta iya yin haka, mutane za su rage fita katare domin ganin Likita. Ministan ya na ganin cewa hakan zai jawowa asibitocin gida jama’a.

A shekarar bara ne shugaba Buhari ya nada tsohon shugaban hukumar NIWA mai kula da hanyoyin ruwan Najeriya, Sanata Olorunnibe Mamora a matsayin Ministansa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel