Bayan Rashin 'Yan APC 15, Tsohon Sakataren Gwamnatin Zamfara Ya Rasu

Bayan Rashin 'Yan APC 15, Tsohon Sakataren Gwamnatin Zamfara Ya Rasu

  • Jam’iyyar APC a Zamfara ta ɗage gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna da aka shirya gudanarwa a Maru
  • Hakan ya biyo bayan rasuwar magoya bayanta 15 a wani haɗarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gangamin jam’iyyar
  • Haka kuma, jam’iyyar ta yi alhinin rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zamfara - Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna ta APC a Zamfara ya yi jimami kan hatsarin mota da aka samu a jihar.

Kwamitin ya sanar da ɗage gangamin da ta shirya gudanarwa a ƙaramar hukumar Maru a ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026.

APC ta yi jimamin rashin tsohon sakataren gwamnati
Taswirar jihar Zamfara da yan APC 15 suka mutu a hatsarin mota. Hoto: Legit.
Source: Original

An yi manyan rashe-rashe a Zamfara

Matakin ya biyo bayan rasuwar magoya bayan jam’iyyar guda 15 a wani haɗarin mota da rasuwar tsohon Sakataren Gwamnati, Alhaji Kabiru Balarabe, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Mutane sun yi rugu rugu da tawagar APC ta yi hadari, an rasa rayuka da yawa

Magoya bayan jam’iyyar sun rasu ne yayin da suke tafiya daga Gummi zuwa Talata Mafara domin halartar ƙaddamar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC a ranar Litinin.

Wasu mutane da dama sun jikkata a haɗarin, kuma a halin yanzu suna samun kulawar likitoci.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Litinin, Babban Sakataren Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen, Malam Abubakar M. Nakwada, ya ce majalisar tana cikin alhini sakamakon waɗannan rashe-rashen da suka faru.

Majalisar ta kuma yi jimamin rasuwar Alhaji Kabiru Balarabe, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Sakataren Gwamnatin jihar kuma fitaccen mutum a Zamfara. Ya rasu ne bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

Nakwada ya bayyana cewa majalisar ta ɗage gangamin da aka shirya yi a Maru domin girmama waɗanda suka rasu tare da nuna goyon baya ga iyalansu da ke cikin jimami.

Sanarwar ta ce:

“Domin girmama waɗanda suka rasu da kuma nuna goyon baya ga iyalan da ke cikin alhini, majalisar ta ɗage gangamin da aka shirya gudanarwa a ƙaramar hukumar Maru ranar Talata, 24 ga Nuwamba, 2026. Za mu sanar da sabon jadawalin gangamin nan gaba.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake dawo da alkawarin da ya dauka a baya, ya roki yan Najeriya

Ya ƙara da cewa majalisar ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan, al’ummar Gummi da kuma daukacin mutanen Zamfara.

A cewarsa, suna bibiyar halin da waɗanda suka jikkata suke ciki, kuma za su ba su tallafin da ya dace tare da taimaka wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Nakwada ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa mamatan kura-kuransu, Ya shigar da su Aljannatul Firdaus, Ya ba waɗanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa, sannan Ya ba iyalan mamatan haƙurin jure wannan babban rashi.

Ɗage gangamin ya zo ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na APC a Talata Mafara.

Gangamin ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyyar, ciki har da tsoffin gwamnonin Zamfara, Abdul’aziz Yari, Ahmad Sani Yarima da Mahmud Aliyu Shinkafi.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.