Gwamnatin Kano ta bada lambobin waya saboda barkewar annoba a jiha
Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya fitar da wasu lambobin wayar salula da za a kira da zarar an ji wani labari game da cutar coronavirus a jihar.
Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana wadannan akwatunan waya ne a wani jawabi da ya fitar a Ranar Asabar. Kwamishinan yada labarai ya fitar da wannan jawabi jiya.
Kamar yadda mu ka samu labari daga The Nation, gwamna Abdullahi Ganduje ya bukaci mutanen Kano su tuntubi wadannan lambobi a duk inda aka yi zargin cutar ta ratsa.
Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, shi ne ya fitar da wannan jawabi a madadin gwamnan, ya na kira ga jama’an jihar Kano su yi hattara.
Malam Muhammad Garba ya bukaci mutanen Gari su yi amfani da wadannan akwatun lambar waya domin su tsare rayuka da lafiyar miliyoyin mutanen da ke jihar Kano.
KU KARANTA: Coronavirus: An killace mutane 39 a Jihar Ogun - Segun Soyoye
Gwamnatin jihar Kano, ta kuma yi kira ga Mazaunan jihar da su bi matakan da ma’aikatar lafiya ta gindaya domin kare kai daga kamuwa da wannan cuta ta coronavirus.
Abdullahi Ganduje ba ya son ganin wannan cuta da ta fito daga kasar Sin ta samu gindin zama a Kano, ganin cewa an killace wasu mutanen kasar ta Sin a jihar Filato.
A jihar Filato mai makwabtaka da jihar Kano, akwai mutanen kasar Sin har uku da ke tsare yanzu a hannun Malaman asibiti bisa zargin cewa su na dauke da wannan cuta.
Lambobin da gwamnatin Kano ta fitar ta hannun Kwamishinan yada labarai su ne:
1. Dr. Imam Wada Bello, Darektan hukumar kula da maganin cututtuka, 08050303343;
2. Dr. Bashir Lawan Muhammad, Akwatin kar-ta-kwana (EOC) na jihar Kano, 08099973292;
3. Sulaiman Ilyasu, hukumar da ke lura da barkewar cuta a Kano (SDSNO), 08039704476;
4. Shugaban hukumar lafiya ta Duniya (WHO) na jihar Kano, 08037038597;
5. Dr. Sharif Yahaya Musa, Darektan hukumar kula da yaduwar cututtuka na Kano, 08176677497
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng