Patrick Kibe: Mutumin da ya zama kwararren likitan ido bayan daukar lokaci yana aikin shara a asibiti

Patrick Kibe: Mutumin da ya zama kwararren likitan ido bayan daukar lokaci yana aikin shara a asibiti

Labarin Patrick Kibe zai bawa mutane damar yadda da cewa aiki tukuru da kuma jajircewa suna sanyawa mutum ya zama wani abu a rayuwa, musamman shi labarin shi da ya fara a 1990, lokacin da yayi tunanin cewa zai zama fasto ne

Ya tattara kayan shi, ya shiga makarantar koyon Bible a Kijabe, amma kuma wannan buri na shi na zama fasto ya samu cikas, inda hakan ya sanya dole ya bari ya fara aikin shara da goge-goge a asibitin Kijabe domin ya samu na sanyawa a bakin salati.

A wani rubutu da shafin asibitin na Facebook suka wallafa, sun bayyana cewa aikin Kibe shine ya dinga sharewa da kuma goge bangaren Wairegi da Salome, bai san cewa watarana mutane za su dinga yi masa layi ba domin ya duba lafiyarsu.

Patrick Kibe: Mutumin da ya zama kwararren likitan ido bayan daukar lokaci yana aikin shara a asibiti

Patrick Kibe: Mutumin da ya zama kwararren likitan ido bayan daukar lokaci yana aikin shara a asibiti
Source: Facebook

Likitan idon ya samu karin girma zuwa mai kula da kayayyaki a asibitin watanni shida bayan yayi aiki a matsayin mai shara da goge-goge, hakan duka na da nasaba da jajircewar shi.

Aikin Kibe a wancan lokacin shine ya dinga lura da magunguna da sauran kayan aikin asibiti.

"Wata rana asibitin ya samu kayan tallafi daga wata babbar kungiya ta duniya, a lokacin da aka kawo kayan, sai na shirya su yadda ya kamata, dana kai rahoton yadda na shirya kayan, sai yayi daidai da yadda kungiyar ta kawo," ya sanarwa da Citizen TV.

KU KARANTA: Majalisar dattawa ta gabatar da kudurin da zai hana amfani da injin janareto a Najeriya

A wannan lokacin ne likitocin asibitin suka gano cewa yana da jajircewa suka bukaci ya shiga makarantar koyon aikin lafiya ta Kijabe, wato Kijabe School of Nursing a shekarar 1993.

Bayan kammala karatun shi, asibitin sun tura shi zuwa Kajiado, inda ya dinga kula da wanni fanni, wannan shine farkon sabuwar rayuwa a gare shi.

Soyayyar da yake yi na aiki a fannin lafiya ta sanya ya shiga makarantu na lafiya masu yawan gaske a kasar Uganda, Tanzania da kuma Kenya.

Ya kammala karatun jami'a inda ya fita da sakamako mai kyau a fannin tiyatar ido daga Kilimanjaro Christian Medical Clinic.

A karshe Kibe ya koma Kijabe Hospital domin ya fara aiki a bangaren ido. Yanzu haka yana yiwa mutane masu matsalar ido aiki a asibitin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel