Hukumar kiwon lafiya ta duniya, WHO ta bayyana cewa wani babban jami’i dake ofishinta na kasar Iran ya kamu da annobar cutar nan mai suna Coronavirus – Covid-19 da ta addabi al’ummomin duniya gaba daya.
Babban daraktan WHO, Dakta Tedros Ghebreyesus ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru inda yace a yanzu haka jami’in da cutar ta kama yana kwance ba shi da lafiya, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.
KU KARANTA: Karancin albashi: Gwamnatin Jahar Gombe ba za ta biya kananan hukumomin N30,000 ba

Tedros
Source: UGC
Tedros yace a yanzu babu inda cutar ta fi kamari kamar Korea, Italy, Iran da kuma Japan, yayin da ake samun saukinta yaduwarta a kasar China, inda ta fara bayyana, don haka Tedros yace a ranar Litinin ma sai da suka kai magunguna da tallafi ga gwamnatin kasar Iran.
“A ranar 1 ga watan Maris an samu rahotanni 206 a kasar China, shi ne mafi karanci a kasar tun daga ranar 22 ga watan Janairu, guda 8 ne kacal daga wajen lardin Hubei, yayin da a wajen China aka samu bullarta sau 8,739 a kasashe 61 tare da mutane 127 da suka mutu a sanadiyyar cutar.” Inji shi.
Sai dai Tedros ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar kare yaduwar cutar Coronavirus, wanda yace a yanzu shi ne babban aikin dake gaban kasashen duniya, idan har aka ma cutar tsayuwan daka tabbas kasashen duniya za su dakatar da yaduwar cutar.
A wani labarin kuma, Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da bullar annobar cutar Coronavirus a kasar, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta bayyana.
Majiyar ta bayyana cewa cutar ta bulla ne a jikin wani dan kasar Saudiyya da ya fito daga kasar Iran, amma ya biyo ta kasar Bahrain, amma zuwa yanzu an killace shi a asibiti, haka zalika an sauki jinin duk mutanen da ya yi mu’amala da su don gudanar da gwaji.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa