Baturen da ya kawo cutar Coronavirus yayi kokarin guduwa daga inda ake tsare shi a Legas
- Bayan gano mai dauke da cutar Coronavirus a jihar Legas, gwamnatin jihar ta kebe shi tare da adana shi a asibiti
- Amma kuma mara lafiyan yayi korafi a kan halin da aka ajiye shi ciki na zafi da tsananin sauro
- A ranar Juma'a ne yayi kokarin guduwa tare da tabbatar da cewa yana kan bakanshi matukar ba a yi komai a kan halin da asibitin yake ba
Biyo bayan gano mai dauke da muguwar cuta ta Coronavirus a Najeriya tare da kebance mai cutar a asibitin Yaba da ke Legas, wani ma'aikacin Lafiya a ranar Juma'a ya ce mara lafiyan ya fusata kuma ya yi yunkurin guduwa.
Mara lafiyan ya nuna damuwar shi a kan yadda wajen da aka kebance shi yake, wata majiya ta ce.
Wani babban ma'aikacin lafiya da ya yi magana da wakilin jaridar The Punch a ranar Juma'a, ya jajanta yadda wajen yake. Ya ce "hukumomi ba su cika alkawarin da suka dauka ba."
Mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat a ranar Juma'a ya ce gwamnatin jihar ta gina wajen kula da marasa lafiyan kuma wanda aka gano yana dauke da cutar na samun sauki.
Hamzat ya ce, "a dakin da yake, akwai gadaje 100 kuma a halin yanzu gado daya ne aka hau. Muna fatan ba za ta ci gaba da yaduwa ba. A shirye muke kuma muna da kayan aiki. Mara lafiyan yana samun sauki don likitoci sun ce yana samun lafiya."
Amma kuma sai ma'aikacin lafiyan ya sanar da cewa mara lafiyan na korafin zafi da sauro. Hakazalika, ba a tanadarwa ma'aikatan lafiyan kayan kariya ba. Ya ce, "mara lafiyan ya so tserewa jiya Alhamis. Dan kasar Italia din wanda injiniya ne ya fusata da halin da yake ciki. Sauro da zafi duk sun ishe shi. Babu komai a dakin banda gado da wajen ajiye-ajiye. Ya kusan guduwa kuma har yanzu yana barazanar hakan."
KU KARANTA: Musulunci addini ne mai matukar rinjaye shine yasa mutanen duniya suka tsane shi - Karen Armstrong
Majiyar ta ce babu wani shiri da jihar Legas din tayi a kan wannan cutar.
Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, gwamnatin jihar Legas din ba ta da wajen adana wadanda suka yi mu'amala da mutumin da ke dauke da cutar.
Kamar yadda majiyar ta sanar, waje daya ne aka tanadar don adana wadanda ake zargi suna dauke da cutar da kuma wadanda aka tabbatar da cewa suna dauke da ita. A hakan kuwa gyaran wajen ake yi don bai kammala ba.
Majiyar ta zargi cewa, dakin an kwashe marasa lafiya daga ciki ne kuma an kange dakin ne da jan kyalle.
A lokacin da aka tambayi wata ma'aikaciyar jinya dalilin da yasa take sanye da abin rufe fuska da kuma safar hannu, sai ta ce "mene ne cutar Coronavirus"?
Amma kuma shugaban asibitin Yaba din, Dr. Abimbola Bowale ya tabbatar da cewa mara lafiyan na samun sauki kuma maganin yana amfani.
Ya ce mara lafiya da aka kawo a ranar Alhamis an kebe shi amma babu wasu manyan alamun cutar da yake nunawa. Ana kuma kula da shi ne kamar yadda dokar lafiya ta tanadar.
"Zamu bibiya sannan mu gano duk mutanen da yayi mu'amala da su kafin nan. Ana ci gaba da binciken kuma komai na zuwa da sauki." Ya ce.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng