Zaben Kano: Maganar Abba Ta Jawo ana So Tinubu Ya Sauka ko a Tsige Shi
- ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus ko kuma Majalisar Tarayya ta tsige shi kan zargin katsalandan a hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan Kano na 2023
- Jam’iyyar ta yi zargin cewa Tinubu ya yi amfani da matsayinsa wajen samun hukuncin da ya amfanar da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya sauya sheƙa zuwa APC
- ADC ta ce hirar da Gwamna Yusuf ya yi da BBC Hausa ta tayar da tambayoyi kan ’yancin bangaren shari’a da kuma yiwuwar amfani da hukuncin kotu wajen cinikin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus ko kuma Majalisar Tarayya ta fara shirin tsige shi bisa zargin katsalandan a hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan Jihar Kano na 2023.

Kara karanta wannan
'Yan Kwankwasiyya sun tunkari Gwamna Abba kan zarge zargen da ya ɗora wa Kwankwaso
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, jam’iyyar ta ce hirar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi da BBC Hausa ta haifar da manyan tambayoyi kan ’yancin bangaren shari’a.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ADC ta yi zargin cewa shugaban ƙasar ya yi amfani da ofishinsa wajen yin tasiri a hukuncin kotu domin samun wata ribar siyasa, bisa yarjejeniyar da ta danganta da sauya shekar gwamnan zuwa APC.
Zargin da ADC ta yi wa Tinubu
Jam’iyyar ta bayyana zargin a matsayin babban saɓa wa rantsuwar kama aikin shugaban ƙasa, inda ta ce babu abin da ya fi muni ga shugaban da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya kamar mayar da shari’a hanyar cinikin siyasa.
A cewar ADC, abin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana a hirarsa ya nuna cewa Tinubu ya samu hukuncin da ya amfanar da shi daga Kotun Ƙoli domin gwamnan ya koma jam’iyyar APC.
Jam’iyyar ta ce irin wannan zargi yana barazana ga bin doka da oda, ’yancin bangaren shari’a da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.
ADC ta nemi a tsige Tinubu
ADC ta yi kira ga Majalisar Tarayya da ta binciki zargin yarjejeniyar, tare da tilasta wa duk waɗanda ake zargin suna da hannu su gabatar da hujjoji.
Vanguard ta wallafa cewa ta kuma buƙaci majalisar ta fara matakan tsige shugaban ƙasa idan aka tabbatar da zargin da take yi masa.

Source: Facebook
Jam’iyyar ta gargaɗi cewa idan aka tabbatar da katsalandan ɗin, hakan zai rage amincewar jama’a da Kotun Ƙoli, tare da aika mummunan saƙo ga masu zuba jari na ƙasashen waje kan yadda doka ke aiki a Najeriya.
ADC ta jaddada cewa Kotun Ƙoli ba wani reshe ba ne na sakatariyar jam’iyyar APC, haka kuma shugaban ƙasa ba shi ne mamallakin bangaren shari’a ba.
Obi ya yi zargin za a bata shi
A wani labarin, kun ji cewa ofishin yaɗa labaran Peter Obi ya yi gargaɗi kan wani zargin shirin farfaganda da ake yi domin danganta tsohon gwamnan da ƙungiyar IPOB.
Ofishin ya ce wasu ’yan jam’iyyar mai mulki da wasu ’yan adawa na ƙoƙarin amfani da batun domin hana ’yan Arewa goyon bayan haɗakar siyasar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.
Obi ya buƙaci kafafen yaɗa labarai su tabbatar da sahihancin duk wani rahoton siyasa kafin wallafa shi, musamman waɗanda ka iya haddasa rabuwar kai a ƙasar.
Asali: Legit.ng
