Gwamnatin Kaduna Ta Yi Niyyar Sayan Abba Hikima, Lauyan Ya Watsa Mata Kasa a Ido
- Lauya kuma mai fafutuka, Abba Hikima, ya ƙi amincewa da filin da gwamnatin Kaduna ta ware masa
- Hikima ya ce ana fuskantar matsin lamba, kama-kama da zargin tsangwama ga mambobin ƙungiyarsa ta Tinubu Must Go
- Ya buƙaci gwamnatin Uba Sani ta bai wa ’yan adawa damar gudanar da siyasa cikin ’yanci, kamar yadda take bai wa APC mai mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Wani lauya kuma mai fafutukar siyasa daga Kano, Abba Hikima, ya ƙi karɓar fili mai girman murabba’in mita 750 da aka ba shi.
Abba Hikima ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ce ta ware masa da ya ce hakan na iya haifar da rashin dacewa a lokacin da yake zargin ana gallaza wa mambobin ƙungiyarsa a jihar.

Source: Facebook
Hikima, wanda shi ne jagoran ƙungiyar Tinubu Must Go Movement (TMG), ya bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Yadda aka ba Abba Hikima kyautar
Ya ce an miƙa masa takardun mallakar filin ne a ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ta hannun wani mutum, duk da cewa bai taɓa neman a ba shi fili ba.
Lauyan ya ce yana godiya da wannan karamci da gwamnatin jihar ta nuna masa, amma yanayin da aka yi hakan da kuma lokacin da aka zaɓa sun haifar masa da damuwar da'a, musamman ganin yadda dangantakar hukumomin jihar da mambobin ƙungiyarsa ta yi tsami.
A cewarsa, Kaduna na daga cikin jihohin da ƙungiyar TMG da mambobinta ke fuskantar manyan ƙalubale wajen gudanar da ayyukansu, ciki har da kama wasu mambobi da zargin tsoratarwa da gallazawa.
Ya kuma bayyana cewa matsalolin sun shafi har da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓe, inda ya ce wasu masu buga kaya a jihar na fuskantar matsaloli na musamman idan suka nemi buga rigunan da tambarin ƙungiyar.
Hikima ya ce irin wannan matsala ba ta faruwa da ƙungiyarsu a sauran jihohin ƙasar.
A cikin bayaninsa, ya ce:
“A irin wannan yanayi, karɓar fili na kashin kai daga wannan gwamnati a irin wannan lokaci zai haifar da rikicin muradin kai wanda ba za a amince da shi ba. Hakan kuma zai iya kawo cikas ga ’yancina na yin magana da ɗaukar mataki kan waɗannan batutuwa.”

Source: Facebook
Godiyar da Abba Hikima ya yi ga Uba Sani
Duk da ƙin karɓar filin, Abba Hikima ya nuna godiya ga Gwamnan Kaduna, Uba Sani, bisa wannan karamci da ya nuna masa.
Sai dai ya bukaci gwamnatin jihar da ta samar da yanayin siyasa mai adalci, inda ’yan adawa za su samu damar gudanar da ayyukansu ba tare da fuskantar tsangwama ba.
Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da cewa ayyukan jam’iyyun adawa, ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma bayyana rashin amincewa cikin lumana suna samun kariya da kulawa iri ɗaya da wadda jam’iyyar APC mai mulki ke samu.

Kara karanta wannan
Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta
Abba Hikima ya magantu kan takarar Gwarzo, Pantami
Mun ba ku labarin cewa lauya Abba Hikima, ya buƙaci INEC ta nemi afuwar Isa Ali Pantami, Aminu Gwarzo da sauran ’yan takarar da ta cire sunayensu.
Ya ce hukumar INEC ta jefa ’yan takarar da magoya bayansu cikin damuwa saboda rashin gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Abba ya bukaci INEC ta biya waɗanda abin ya shafa diyya saboda kuɗaɗen da suka kashe wajen shigar da ƙara.
Asali: Legit.ng

