Dattijon Dan Fim a Najeriya Ya Rasu bayan Fama da Jinya a Asibiti

Dattijon Dan Fim a Najeriya Ya Rasu bayan Fama da Jinya a Asibiti

  • Rahotanni sun nuna cewa fitaccen jarumin fina-finan Najeriya, Pete Edochie, ya rasu yana da shekaru 79 a duniya
  • Edochie ya rasu ne da misalin ƙarfe 12:30 na daren Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, a Enugu bayan fama da cutar kansa
  • Ɗansa, Leo Pete Edochie, ne ya sanar da rasuwar a madadin iyalansa, ta cikin wata sanarwa da ya wallafa cikin daren

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Fitaccen jarumin fina-finai kuma tsohon mai gabatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin a Najeriya, Chief Pete Edochie, ya rasu yana da shekaru 79.

Sanarwar da ɗansa, Leo Pete Edochie, ya fitar a madadin iyalansa ta bayyana cewa jarumin ya rasu ne a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026, bayan fama da cutar kansa.

Kara karanta wannan

'Na leƙo jahannama': Paparoma ya faɗi adadin lokutan da ya ga sheɗan da idonsa

Pete Edochie da ya rasu
Jarumin fim da ya rasu, Pete Edochie. Hoto: Leo Edochie
Source: Instagram

Punch ta wallafa cewa iyalansa sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi, tare da addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.

Yadda aka sanar da rasuwar Edochie

A cikin sanarwar, iyalan marigayin sun bayyana shi a matsayin miji, uba, ɗan’uwa kuma ɗan gida da suke matuƙar ƙauna.

Sanarwar ta ce Pete Edochie ya rasu da misalin ƙarfe 12:30 na dare a Enugu, bayan fama da rashin lafiya na tsawon lokaci.

Ya fito ne daga Akamnato, Ifite Nteje, da ke Jihar Anambra. Ya rasu ya bar matarsa, Josephine Edochie, ’ya’yansa, ’yan’uwansa da sauran dangi.

Rahotanni sun nuna cewa iyalansa sun ce za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa nan gaba.

Rawar da ta sa Edochie shahara

Pete Edochie na cikin fitattun jaruman fina-finan Najeriya, musamman saboda yadda yake taka rawar dattawa da shugabannin iyalai a fina-finai.

Ya samu karbuwa sosai a Najeriya da sauran ƙasashe bayan taka rawar Okonkwo a fim ɗin talabijin na Things Fall Apart, wanda Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) ta shirya a shekarar 1987.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe malamai 2, sun yi awon gaba da mutane sama da 10

Fim ɗin ya samo asali ne daga littafin marubucin Najeriya, Chinua Achebe, mai suna Things Fall Apart.

Wannan rawa ta ƙara fito da bajintarsa a harkar fim, tare da sa masu kallo a wajen Najeriya su san da shi.

Aikinsa kafin zama jarumin fim

Rahotanni sun bayyana cewa kafin ya shahara a masana’antar fina-finai, Edochie ya fara aikinsa ne a fannin watsa shirye-shirye.

Ya fara aikin mai gabatar da shirye-shirye a shekarar 1967, kafin daga bisani ya koma harkar fim, inda ya shafe shekaru da dama yana taka rawa a fina-finan Najeriya.

Pete Edochie
Fitaccen jarumi, Pete Edochie. Hoto: Leo Pete Edochie
Source: Instagram

Gudummawar da ya bayar ga masana’antar nishaɗi ta sa aka karrama Pete Edochie da lambar yabo ta ƙasa ta MON.

'Yan APC sun rasu a Zamfara

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar APC a Zamfara ta ɗage gangamin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna da aka shirya gudanarwa a Maru.

Matakin ya biyo bayan rasuwar magoya bayan jam’iyyar 15 a wani haɗarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa gangamin.

Haka kuma, jam’iyyar ta yi alhinin rasuwar tsohon Sakataren Gwamnatin Zamfara, Alhaji Kabiru Balarabe da ya rasu bayan shafe shekaru yana aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng