'Tinubu Ya Goyi Baya na Kare Kasar Yarabawa daga 'Yan Ta'adda,' Sunday Igboho
- Shugaba Bola Tinubu ya umarci Sunday Igboho da ya taimaka wajen tabbatar da tsaro a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
- Tinubu ya bukaci rundunar tsaron Iru Ekun da ta hada kai da jami’an tsaro domin dakile shigowar ’yan ta’adda daga kasashen Afirka
- Igboho ya ce shugaban kasar ya ba shi umarnin kare dazuzzuka, kauyuka da biranen yankin daga barazanar tsaro da ka iya tasowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci dan gwagwarmayar kare muradun Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, da ya taimaka wajen tabbatar da tsaro a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Tinubu ya kuma jaddada muhimmancin hadin gwiwar rundunar tsaron Iru Ekun da rundunar ’yan sanda, sojojin Najeriya, hukumar DSS da sauran hukumomin tsaro domin dakile matsalar rashin tsaro.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta ruwaito cewa ofishin yada labaran Igboho ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, ranar Litinin.
Me Tinubu ya tattauna da Igboho?
Sanarwar ta ce Tinubu ya gana da Igboho a cikin motarsa jim kadan bayan kammala gangamin yakin neman zabensa na shugaban kasa karkashin jam’iyyar APC a dandalin Mapo Hall da ke Ibadan ranar Asabar.
Tattaunawar ta shafi ayyukan rundunar Iru Ekun da bukatar jami’anta su hada kai da hukumomin tsaro domin inganta zaman lafiya a kauyuka da birane.
Vanguard ta wallafa cewa Igboho ya ce shugaban kasar ya bukace shi da ya ci gaba da ayyukansa na tabbatar da tsaro tare da hukumomin da abin ya shafa.
An bukaci kare dazuzzuka
A cewarsa, Tinubu ya umarci rundunar Iru Ekun da ta sanya ido kan dukkan yankuna, musamman dazuzzuka da wuraren da ake noma, domin hana shigowar ’yan ta’adda daga kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.

Kara karanta wannan
Abin da ya rage a ƙaddamar da ƴan sandan jihohi a Najeriya duk da ƙorafin ƴan adawa
Ya ce shugaban kasar ya ambaci kasashen da ke kusa da Tafkin Chadi da Mali da sauran kasashen Afirka a matsayin wuraren da ka iya zama tushen shigowar ’yan ta’adda.
Igboho ya bayyana cewa tattaunawar ta dauki kusan mintuna biyar, inda shugaban kasar ya nuna muhimmancin hada kai da hukumomin tsaro wajen dakile laifuffuka.

Source: Facebook
Sanarwar ta ambato Igboho yana cewa Tinubu ya kuma umurci rundunar da ta kare dukkan ’yan Najeriya da ke yankunan da take aiki, ba tare da la’akari da kabila, addini ko jam’iyyar siyasa ba.
Ya kara da cewa shugaban kasar ya jaddada bukatar sanar da hukumomin tsaro tun da wuri kafin daukar matakai, domin samun nasarar ayyukan da kuma dawo da amincewar jama’a ga gwamnati wajen kare rayukansu.
Kiran Tinubu ga Igbo
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya nemi goyon bayan ’yan kasuwar Igbo, dattawa da shugabannin al’ummarsu da ke Legas gabanin zaben shugaban kasa na ranar 16 ga Janairun 2027.
Tinubu ya yi alkawarin tafiyar da gwamnati mai bai wa dukkan kabilu dama, inda ya bayyana farin cikinsa da yawan mutanen da suka halarci taron da aka shirya domin tattaunawa da shugabannin Igbo.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce shugababan ya bayyana hakan ne a wani taron da kungiyar Ndigbo ta shirya a cibiyar Wole Soyinka da ke Iganmu, jihar Legas.
Asali: Legit.ng
