Martanin Sarkin Musulmi game da Hari kan Rarara da Tinubu a Masallaci
- Hukumar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi Allah wadai da hare-haren da wasu mutane ke kai wa masallatai a sassan ƙasar
- Sakatare-Janar na NSCIA, Is-haq Oloyede, ya ce kai hare-hare a masallatai ya saɓa wa koyarwar Musulunci, kuma ba za a amince da shi ba
- Hukumar ta gargaɗi Musulmi kan amfani da bambancin fahimtar addini ko siyasa wajen haddasa rikici, musamman yayin da ake shirin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Hukumar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta yi Allah wadai da hare-haren da wasu mutane ke kai wa masallatai da kewayensu a sassan ƙasar.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a Abuja ranar Litinin, Is-haq Oloyede, sakataren-janar na hukumar, ya bayyana hare-haren a matsayin abin ƙyama da ya saɓa wa koyarwar Musulunci.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Mutane da dama sun mutu da aka yi yunkurin kashe sanata a wurin kamfe

Source: Twitter
Gargadin da aka yi wa ƴan Najeriya
Oloyede ya yi gargaɗin cewa bai kamata a riƙa amfani da bambancin fahimtar addini ko saɓanin siyasa a matsayin hujjar aikata tashin hankali ba, cewar TheCable.
Ya ce NSCIA na kallon duk wani nau'in ƙiyayya, musamman a cikin masallatai, a matsayin mummunan aiki da ya saɓa wa koyarwa, ƙa'idoji da ruhin Musulunci.
Ya ƙara da cewa wannan mummunan aiki ne da duk Musulmin da ke neman yardar Allah Maɗaukakin Sarki ya kamata ya guje masa.
Yayin da 'yan Najeriya ke shirin gudanar da zaɓen 2027, hukumar ta jaddada cewa masallaci ba gini kawai ba ne.
Ta ce masallaci wuri ne mai tsarki, mafakar ibada da zaman lafiya, inda ake ambaton Allah, yin tunani na addini, ƙarfafa 'yan'uwantakar Musulunci da koyar da addini.
Hukumar ta bayyana cewa koyarwar Musulunci ta tanadi kare martabar masallatai, da rayuka, mutunci da tsaron dukkan mutanen da ke gudanar da ibada a cikinsu.

Kara karanta wannan
Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da matar da ake zargin Sarkin Daura ya taɓa jikinta
Sakataren-janar na NSCIA ya kawo wasu ayoyin Alƙur'ani da koyarwar Annabi Muhammad (SAW) domin jaddada muhimmancin kare wuraren ibada da rayukan bil'adama.
Oloyede ya ce waɗannan koyarwa ba su yarda da tashin hankali, tsoratarwa, cin zarafi, farmaki ko barazana ga rayukan mutane saboda bambancin fahimtar addini ko saɓanin siyasa ba.
Ya ƙara da cewa babu wani dalili, ko na addini, siyasa ko matsalolin tattalin arziki da zai halatta tauye tsaron mutane ko kai musu hari.
Ya bayyana cewa dukkan Musulmi na da 'yanci da haƙƙoƙi iri ɗaya a cikin masallaci, don haka bai kamata a take haƙƙin wani mai ibada ba.

Source: Twitter
Bukatar hukumar ga al'ummar Musulmi
Oloyede ya buƙaci Musulmi su riƙa warware matsalolinsu ta hanyar tattaunawa, shawarwari masu amfani, bin doka, zuwa kotu da sauran hanyoyin da doka ta amince da su.
Haka kuma, ya yi kira ga shugabannin masallatai da su taimaka wajen kama mutanen da suka aikata laifukan da suka saɓa wa tsarkin wuraren ibada.
Ya kuma buƙaci shugabannin su tattara faifan bidiyo na irin waɗannan abubuwa tare da miƙa su ga jami'an tsaro domin gudanar da bincike da ɗaukar matakin da ya dace.

Kara karanta wannan
Abin da matasa suka yi wa Dauda Kahutu Rarara a masallacin Abuja ya fusata jigon APC
Bugu da ƙari, ya yi kira ga 'yan siyasa, shugabannin addinai da na al'umma, da sauran jama'a su yi taka-tsantsan wajen furuci da ayyukan da ka iya ƙara rura wutar rikici, cewar Punch.
Ya ce ya kamata masu hannu a irin waɗannan ayyuka su dakatar da cin zarafin masallatai ta hanyar tashin hankali, tare da guje wa abubuwan da za su jawo wa ƙasar kunya.
Hari kan Rarara: An bukaci taimakon Sarkin Musulmi
An ji cewa kungiyar matasan Arewa (NEYGA) ta nemi Sultan Sa’ad Abubakar ya shiga tsakani kan zargin amfani da masallatai wajen siyasa.
Ta yi Allah wadai da hare-haren da aka kai wa mawaƙin siyasa Dauda Kahutu Rarara a Masallacin Ƙasa da ke Abuja yayin sallar Juma’a.
NEYGA ta kuma buƙaci shugabannin JNI da MURIC su ɗauki mataki domin dakile siyasantar da masallatai da kare zaman lafiya a Arewa.
Asali: Legit.ng