Coronavirus: Kwamishinan lafiyan jihar Legas ya bayyana sakamakon gwajin mutum 3

Coronavirus: Kwamishinan lafiyan jihar Legas ya bayyana sakamakon gwajin mutum 3

- Dukkan mutane uku da aka gwada akan zargin suna dauke da cutar coronavirus a jihar Legas an gano basu da ita

- Akin Abayomi, kwamishinan lafiyan jihar Legas, ya bayyana hakan a sakon da ya fitar a shafinsa na Twitter a yammacin yau Juma’a

- Najeriya ta samu mai cutar ne kusan mako daya da ya gabata bayan isowar wani mutum daga kasar Italiya daga birnin Milan

Dukkan mutane uku da aka gwada ana zargin su dauke da cutar coronavirus a jihar Legas an gano basu da ita. An killace mutanen uku ne a asibitin na musamman da ke yankin Yaba a jihar Legas.

Akin Abayomi, kwamishinan lafiyan jihar Legas ya bayyana hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Twitter a yammacin yau Juma’a.

Abayomi ya ce dukkansu babu mai dauke da cutar.

“Dukkan mutane ukun da aka zarga suna dauke da cutar Covid19 ba su dauke da ita. Matafiya ne daga kasar Faransa, Ingila da kuma China. An dau jininsu don bincike a jiya kuma an gano cewa basu dauke da cutar. Daga nan kuwa muka sallamesu.” kwamishinan yace.

Coronavirus: Kwamishinan lafiyan jihar Legas ya bayyana sakamakon gwajin mutum 3
Coronavirus: Kwamishinan lafiyan jihar Legas ya bayyana sakamakon gwajin mutum 3
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban

Wannan na bayyana cewa mutum daya aka samu mai dauke da cutar a Najeriya. Cutar kuwa ta kashe sama da mutane 3,000 inda ta shafi mutane a kalla 100,000 a fadin duniya.

Najeriya ta samu mai cutar ne kusan mako daya da ya gabata bayan isowar wani mutum daga kasar Italiya daga birnin Milan.

An gano cewa mara lafiyan ya kama dakin otal ne a kusa da filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas. A washegarin ranar 24 ga watan Fabrairun ne ya karasa Ewekoro da ke jihar Ogun,

An gano cewa alamun cutar ta fara bayyana a tare da shi ne kafin a yi masa gwajin cutar tare da killace shi a asibiti a jihar Legas.

Daga baya ne gwamnatin ta sanar da cewa ta gano mutane 38 da suka yi mu’amala da mai cutar kuma an tsamosu tare da killacesu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164