'Yan gidan sarautar Saudiyya sun sha zuwa Najeriya a duba lafiyarsu - Ministan Lafiya
Karamin ministan lafiya, Olorunnimbe Mamora, ya ce a baya Najeriya ta ci moriyar shigowar bakin haure da ke zuwa don a duba lafiyarsu.
Da ya ke bayyana hakan ranar Litinin a Abuja, ministan ya ce baki daga kasashen duniya su kan shigo Najeriya a baya domin a duba lafiyarsu.
A cewar ministan, "a shekarun 50s da 60s, Najeriya ta ci moriyar shigowar baki, da suka hada da 'yan gidan sarautar Saudia, da ke zuwa asibitin koyar wa na jami'ar Ibadan domin a duba lafoyarsu."
"Wasu na fita kasashen ketare don a duba lafiyarsu saboda karancin kayan aiki a asibitocinmu na gida. Dole mu tabbatar mun samar da kayan aiki na zamani a asibitocinmu idan mu na son 'yan kasa su e tsaya wa ana duba lafiyarsu a Najeriya.
"Alhakinmu ne, a matsayinmu na kasa, mu tabbatar da cewa mun inganta bangaren lafiya domin amfanin dukkan 'yan kasa.
DUBA WANNAN: EFCC ta cafke wata mata da ta damfari Hadiza Inna Sanusi N36m a Kano
"Da zarar mun yi hakan za a samu raguwar yawan fita kasashen ketare da 'yan Naeriya ke yi domin a duba lafiyarsu."
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng