Dalilinmu na gayyato dan kasar Italiya mai cutar 'Corona Virus' Najeriya - Kamfanin Lafarge

Dalilinmu na gayyato dan kasar Italiya mai cutar 'Corona Virus' Najeriya - Kamfanin Lafarge

A yayin da cutar 'Corona Virus' ke cigaba da shiga kasashen duniya, kamfanin siminti na 'Lafarge Africa Pls' da ke jihar Ogun ya bayyana dalilinsa na gayyato baturen kasar Italy da aka gano cewa yana dauke da kwayar cutar.

A jawabin da darekta a kamfanin, Segun Soyoye, ya fitar ya bayyana cewa sun gayyaci baturen zuwa kamfanin ne domin duba yadda aka kafa wasu injina da aka sayo daga kasar Sweden.

Soyoye ya bayyana hakan ne a harabar kamfanin yayin wata ziyarar gani da ido da jami'an cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) da na hukumar lafiya ta duniya (WHO) suka kai masana'antar.

Darektan ya shaidawa tawagar bakin cewa gidan da baturen ya sauka yana da nisan kilomita biyar daga wurin aikin kamfanin.

"Dan kasar Italiyan ya ziyarci Najeriya ne domin dalilin kasuwanci. Ya sauka a jihar Legas ranar Litinin, kuma ya kwana a Otal din filin jirgin sama na Legas da ke yankin Ikeja. Direbanmu ya kai shi wurin. Mun gaggauta sanar da shugaban kamfaninmu halin da bakon ke ciki bayan mun fuskanci yana cikin yanatin rashin koshin lafiya. Sai da muka tabbatar da cewa duk wanda ya yi wata hulda da su an tafi da su domin a gwada su," kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa Soyoye ya fada.

Dalilinmu na gayyato dan kasar Italiya mai cutar 'Corona Virus' Najeriya - Kamfanin Lafarge
Kwayar cutar 'Corona Virus'
Asali: Twitter

Jami'an gwamnati sun bayyana cewa ya zuwa yanzu akwai mutane 39 da aka kebe su a wata cibiya domin duba lafiyarsu bayan an tabbatar da cewa sun gana da baturen bayan zuwansa Najeriya.

DUBA WANNAN: Sheikh Pantami ya bawa malamai masu sukar hana bara a Kano muhimmiyar shawara

Kazalika, gwamnatin jihar Ogun da mahukuntan kamfanin sun karyata jita-jitar da ke yadawa a gari a kan cewa an rufe kamfanin sakamakon gayyato baturen da ya kawo kwayar cutar 'Corona' Najeriya.

Kwamishinan lafiya a jihar Ogun, Tomi Coker, da shugaban tawagar ma'aikatan WHO, Ibrahim Mamadu, sun yaba wa mahukuntan kamfanin Lafarge bisa daukan matakin gagga wa domin dakile yaduwar kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel