An tabbatar da samun cutar Coronavirus a jikin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro
- Wani gwaji da aka gabatar akan shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya tabbatar da cewa yana dauke da cutar Corona mai kisa
- An gabatar da gwajin ne bayan an samu cutar a jikin daya daga cikin mataimakansa a gwamnati
- Hakan ya zo ne kwanaki kadan bayan ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump
An tabbatar da shigar cutar Corona jikin shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro.
Dan gidan Bolsonaro, Eduardo shine ya sanar da Fox News yace yanzu haka suna cigaba da gabatar da gwaji a jikin shi domin nemo hanyar da za a bullowa lamarin.
Eduardo ya kara da cewa suna tsammanin fitar sakamako na biyu akan gwajin zai fito nan bada dadewa ba.
An samu sakamakon cutar a jikin nashi ne kwanaki kadan bayan Bolsonaro ya gana da shugaban kasar Amurka Donald Trump a Mar-a-Lago.
Bayan fitar wannan labari a kasar ta Brazil, an kira duka masu fada a ji na kasar, inda suka gabatar da taron gaggawa a ofishin shugaban ma'aikata, kamar yadda Fox News ta ruwaito.
An gabatar da gwajin a jikin Bolsonaro ne bayan daya daga cikin mataimakansa, wanda shima ya halarci wani taro a birnin Florida aka same shi da cutar ta COVID-19.
KU KARANTA: Kisan kiyashin da ake yiwa Musulmai a Delhi ya sanya su barin gidajensu don su tsira da rayukansu
Haka shima sakataren sadarwa na shugaban kasar Fabio Wajngarten, mai shekaru 64 a duniya wanda shi ma ya kai ziyara birnin Miami, an ga alamun cutar a jikinshi, inda aka gabatar da gwaji kuma aka tabbatar da ita a jikinshi.
Wannan dai na zuwa ne bayan Peter Dutton, ministan cikin gida na kasar Australia ya kamu da cutar, bayan ya dawo daga birnin Washington D.C, inda ya gana da Attorney General William Barr da kuma Ivanka Trump.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng