"Abin da Ya Banbanta Tinubu da Buhari, Yar'adua da Sauran Shugabannin Najeriya da Suka Gabata"
- Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana abin da ya banbanta Shugaba Bola Tinubu da shugabannin da suka gabace shi
- Ya ce sake fasslin kasuwar canjin kuɗi, tsaro, gine-ginen ababen more rayuwa, noma da lantarki sun bambanta gwamnatin Tinubu da waɗanda suka gabace ta
- Idris ya ce Najeriya ta kwashe kusan shekaru 40 tana fama da matsalolin tattalin arziki saboda gwamnatocin baya sun kasa magance su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigera - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan ’Yan Ƙasa, Mohammed Idris, ya kare manufofin tattalin arziki da tsafin shugabanci na Shugaba Bola Tinubu.
Ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wahala amma wajibi waɗanda gwamnatocin baya suka guje musu tsawon shekaru.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Muhammad Idris ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi kan ayyukan gwamnatin a wani taron tattaunawa da aka gudanar a Legas.
Idris ya ce gwamnatin Tinubu ta bambanta da waɗanda suka gabace ta ta fuskar kula da kasuwar canjin kuɗi, daidaita ayyukan tsaro, bunƙasa ababen more rayuwa, noma, gyaran wutar lantarki da cire tallafin fetur.
Ta ce Najeriya ta shafe kusan shekaru 40 tana fama da matsalolin tattalin arziki saboda gwamnatoci daban-daban sun kasa magance manyan matsalolin da ke cikin tsarin tattalin arzikin ƙasar.
Ya kawo kasuwar canjin kuɗin waje a matsayin ɗaya daga cikin ɓangarorin da Shugaban Ƙasa ya nuna jarumtar siyasa wajen gyara ta.
Idris ya ce:
“Tsawon shekaru 40 muna ta ƙoƙarin yin hakan amma ba mu yi ba, mun manta da cewa muna da wani gurɓataccen tsarin kasuwar canjin kuɗi a ƙasar nan.
"Masu tsara harkoki, masu harkar takardun jarida, babu wanda ya san yadda zai tsara aikinsa. Farashin da ka samu da safe ya bambanta da wanda za ka samu da rana, haka kuma da na yamma.”
Ya yi iƙirarin cewa gyare-gyaren da gwamnatin ta yi a kasuwar canjin kuɗi sun taimaka wajen magance matsalolin da suka sa tsara harkokin tattalin arziki ya yi wahala, duk da cewa ya amince har yanzu ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale da ya kamata a shawo kansu.
Ya yi magana kan tsaro
Dangane da tsaro, ministan ya ce inganta haɗin gwiwa tsakanin rundunonin soji ya taimaka wajen samun nasarorin yaƙi da ta’addanci da sauran barazanar tsaro.
Ya ce haɗin gwiwa tsakanin hafsan sojin ƙasa, hafsan sojin sama da sauran hukumomin tsaro ya inganta a ƙarƙashin gwamnatin yanzu, lamarin da ya sa ake samun ingantaccen haɗin kai wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Idris ya tuna cewa a baya ’yan Boko Haram sun taɓa mamaye ƙananan hukumomi da dama a Jihar Borno, yana mai cewa yanayin ya sauya sosai.
Ya kuma kawo ingantuwar tsaro a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, wadda a baya ta yi kaurin suna wajen kashe-kashe da satar mutane.
Ya ce wannan ci gaba ya nuna cewa matakan da gwamnati ke ɗauka kan tsaro suna haifar da sakamako, duk da cewa akwai sauran ayyukan da ya kamata a yi.
Kun ji cewa
Asali: Legit.ng

