A 2015 mu ka binciko maganin da zai iya warkar da Coronavirus – Maurice Iwu
Tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya na INEC, Farfesa Maurice Iwu ya na ikirarin cewa Najeriya ta gano maganin cutar Coronavirus tun a shekarar 2015.
Maurice Iwu wanda kwararren Malami ne a bangaren hada magunguna, ya ce shi da Yaransa sun gano maganin da zai warkar da cutar nan ta Covid 19 da ke yawo.
Farfesan ya ce tun 2015 shi da Abokan bincikensa su ka gano maganin da ake tunanin zai warkar da wannan cuta a wani bincike da su ka yi a Najeriya da Amurka.
Maurice Iwu ya ce sun soma wannan bincike ne a Jami’ar Nsukka ta Najeriya, inda daga baya aka cigaba a Amurka lokacin da ya ke aiki a babban birnin Washington.
Kwarraren Shehin ya yi aiki na tsawon lokaci a matsayin Malami kuma Mai bincike a wata cibiya da ke irin wannan nazarin a karkashin gidan Sojin Amurka.
KU KARANTA: Cutar Coronavirus ta shiga kasashe fiye da 60 a kwanaki 60
Maurice Iwu ya yi wannan bayani ne jiya Ranar Litinin, 2 ga Watan Maris, a lokacin da ya gana da Ministan kimiyya da fasahan Najeriya watau Dr. Ogbonnaya Onu.
Bayan haka Farfesa Iwu ya bayyana cewa a lokacin da cutar Ebola ta barke a 2014, shi da yaransa sun riga sun yi bincike game da wannan cutar tun a shekarar 1999.
“Yanzu da Coronavirus ta shigo a 2019 a matsayin cutar Covid19, mun samo maganin da mu ke tunanin zai warkar da cutar tun a shekarar 2015, kuma mun buga.”
Farfesan hada magungunan ya ke cewa akwai bukatar a rika nazarin irin wadannan cututtuka. A na sa jawabin, Ministan kimiyyar, ya yabawa kokarin Maurice Iwu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng