Ministar kiwon lafiya ta kamu da cutar Coronavirus, ta killace kanta

Ministar kiwon lafiya ta kamu da cutar Coronavirus, ta killace kanta

Ministar kiwon lafiya ta kasar Birtaniya, Nadine Dorries ta kamu da cutar coronavirus, kamar yadda ta bayyana da kanta a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 10 ga watan Maris.

Punch ta ruwaito Minista Nadine ta bayyana cewa: “Ina tabbatar da cewa na kamu da cutar Coronavirus bayan gwajin da aka min ya tabbatar da hakan, kuma na fara killace kaina a gida tun da aka gano hakan.” Inji ta.

KU KARANTA: Kowa da matsalarsa: Matashi ya kama hanya a kasa don jinjina ma Sarkin Kano Aminu daga Jigawa

Wannan lamari na Minista Nadine Dorries ya kara kambama tsoro da fargaban da ake fama da shi a kasar Birtaniya na yiwuwar kamuwar manyan jami’an gwamnatin kasar Birtaniya da cutar Coronavirus.

A yanzu haka jami’an kiwon lafiya sun dukufa binciken yadda Nadine ta kamu da cutar, da kuma inda ta kamata, tare da lissafa duk mutanen da suka yi mu’amala da ita tun daga wancan lokaci.

Zuwa yanzu dai mutane 6 sun mutu a sanadiyyar wannan annoba, kuma mutane 370 sun kamu da cutar kamar yadda alkalumma suka tabbatar. Nadine Dorries ce yar siyasar Birtaniya ta farko da ta fara kamuwa da cutar Corona.

Sai dai wasu rahotanni sun tabbatar da kafin cutar ta bayyana a jikin Nadine, ta yi mu’amala da daruruwan mutane, daga ciki har da shugaban kasar Birtaniya, Boris Johnson. Daga ranar Juma’ar da ta gabata ne Nadine ta fara rashin lafiya.

A wani labarin kuma, an daga wasan zakarun kasar Ingila inda kungiyar Arsenal za ta fafata da Manchester City a ranar Laraba biyo bayan tsoron yaduwar cutar Coronavirus.

A yanzu haka dai kungiyar Arsenal ta killace yan wasanta gaba daya da wasu ma’aikatan kungiyar guda hudu biyo bayan mu’amala da suka yi da mamallakin kungiyar Olympiaco na kasar Girka wanda a yanzu haka aka tabbatar cutar ta harbe shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel