A rika wanke hannun da ruwa da sabulu domin kauracewa Coronavirus – Mamora

A rika wanke hannun da ruwa da sabulu domin kauracewa Coronavirus – Mamora

Karamin Ministan kiwon lafiyan Najeriya, Adeleke Mamora, ya yi magana game da cutar nan ta Coronavirus da ta barke a Duniya a farkon shekarar nan.

Ministan ya bayyana cewa wanke hannu da ruwa da kuma sabulu zai taimaka sosai wajen kare jama’a daga kamuwa da wannan mugun ciwo da ke yawo.

Adeleke Mamora ya ba jama’a su tsabtace hannuwansu domin gudun kamuwa da cutar. Ministan ya yi wannan bayani ne a lokacin da aka yi hira da shi dazu.

Da ya ke magana a gidan talabijin Channels TV a Ranar Litinin, 2 ga Watan Maris, Ministan ya ce gwamnatin Najeriya ta na bakin kokarinta game da cutar.

Mamora ya shaidawa ‘Yan jaridar cewa amfani da ruwa da sabulu a cuda hannu, shi ne babbar hanyar da za a bi wajen rigakafin kamuwa da wannan cuta.

KU KARANTA: Wani 'Dan wasan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronovirus

A rika wanke hannun da ruwa da sabulu domin kauracewa Coronavirus – Mamora
Adeleke Mamora ya bukaci mutane su rika wanke hannuwansu da kyau
Asali: Depositphotos

“Wanke hannu da sabulu da ruwa ya na da amfani. A iyaka bakin sani na, wannan shi ne babban abin da ya kamata ayi domin maganin cutar.” Inji Mamora.

Mai girma Ministan ya kuma kara jan hankalin jama’an kasar da cewa: “Tsummar da jama’a su ke rububin saye domin su rufe fuskarsu ba ta zama tilas ba.”

“A iya cewa ba mu da tsarin kiwon lafiya da ya cika dari-bisa-dari a Najeriya, amma za mu cigaba da karfafa tsarin da ke kasar.” Ministan lafiyar ya sha alwashi.

Wannan cuta ta shigo Najeriya ne ta hannun wani Mutumin kasar Italiya da ya shigo Legas. An tabbatar da wannan ne a Ranar Alhamis din da ta gabata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng