Labaran garkuwa da mutane
Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana gaskiyar lamurran da suka kara tabarbarewar tsaro a arewacin Najeriya, inda ya danganta lamarin da yawaitar sace shanu daga Arewa.
Sheikh Ahmad Gumi ya sake magana kan yadda gwamnatin Buhari ke kokari wajen ragargazar 'yan bindiga a yankin Arewa maso yammacin Najeriya, ya ce ba daidai bane.
Wani rahoton fasaha da wata kungiya ta fitar, ya bayyana cewa aƙalla ɗalibai 1,409 ne ɓarayi suka sace daga makarantunsu cikin watanni 19 a faɗin Najeriya.
Yan bindigan da suka jagoranci sace matar fasto a babban birnin tarayya Abuja tare da matarsa sun nemi yan uwa su tattara musu tsabar kuɗi miliyan N50 fansa.
Rundunar 'yan sanda sun shaida cewa, wasu 'yan bindiga sun sace sarkin New Bassa ta jihar Neja, inda tuni aka tura jami'an tsaro da 'yan banga domin ceto sarkin
Wasu 'yan bindiga sun mamaye garin Kurami, inda suka sace iyalan dan majalisar dokoki mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar Katsina. An sace matarsa
Gwamnan jihar Bayelsa ya bayyana cewa, Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro na siyasa baya ga ta 'yan bindiga, tayar da kayar baya da sauran munanan laifuka.
Rundunar 'yan sanda a jihar Neja ta samu nasarar hallaka wasu 'yan bindiga da shugabansu a wani yankin jihar yayin da suke kokarin kai hari wanai kauye a jihar.
A wani sabon harin 'yan bindiga, an hallaka wasu mutane biyu a jihar Kaduna. Sojoji kuwa sun ceto wasu mutane uku da 'yan bindiga suka sace a wani yankin jihar.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari