Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

  • Sheikh Ahmad Gumi ya sake jaddada ra'ayinsa na cewa ya kamata gwamnati ta zauna tattaunawa da 'yan ta'adda
  • A cewarsa, yadda sojoji ke ragargazar 'yan bindiga ba zai zama mafita ga matsalar rashin tsaro a Najeriya ba
  • Ya ce ya kamata gwamnati ta dauki matakan tattaunawa fiye da matakan yakar 'yan ta'adda a yankin Arewa

Kaduna - Babban malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kaiwa kan 'yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.

Malam Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ta shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan 'yan bindiga a dazuzzukan Zamfara.

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

Sanarwar, mai taken: ‘Zamfara: The Flaring of Crisis’, ta jaddada cewa matakin soji kan masu aikata miyagun laifuka “ba mafita bane ko hikima”.

Yadda sojoji ke yakar 'yan bindiga ba zai daidaita lamura ba, inji Sheikh Gumi
Sheikh Ahmad Mahmud Gumi | Hoto: dailytust.com
Asali: Facebook

A cikin sanarwar, Gumi ya bayyana yadda gwamnati ke tafka asara wajen kashe kudade don sayen makamai da jiragen yaki kuma babu wani sauyi a yakar 'yan bindiga, wanda a cewarsa, zai durkusar da tattalin arzikin kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

“Abin takaici, wannan ba mafita bane ko hikima. Lokacin da ba ku da ikon kayayyakin aikin dakile tashin hankali, to tattaunawa tana da ikon warware rikici.
"Wannan shi ne abin da Majalisar Dinkin Duniya ke nufi. watau kudurin daidaita rikice-rikice. Abin da muke gani ya wuce masu 'yan ta'adda da ta'addanci kawai, eh yana iya farawa kamar haka amma kamar kowane rikici, yana da sarkakiya.”

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Gwamnatin Tarayya Ta Saki ‘Yan Boko Haram 100 Daga Kurkuku a Boye

Mutane da dama sun fi bukatar tattaunawa fiye daukar matakan soji

A cikin sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo, Gumi ya kara bayyana cewa, ya tattauna da 'yan bindiga da dama kan yadda za su mika wuya da kuma tattaunawa dasu.

Hakazalika, ya bayyana cewa, ya gana da gwamnoni da shugabanni da yawa, sun kuma tabbatar da zabin tattaunawa da 'yan bindiga fiye da daukar matakan soji.

A cewar sanarwar:

"Na gana da yawancin shugabannin 'yan bindiga don neman mafita daga wannan matsala. Na tattauna da 'yan siyasa da jami'an tsaro. Ban da 'yan kalilan, yawancin gwamnonin jihohi suna son a warware rikicin cikin lumana.
“Yan sanda da sauran jami'an tsaro suma sun fahimci girman matsalar.

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Yyayen daliban da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara, sun koka kan rashin iya jin ta bakin masu garkuwa da mutanen da suka sace 'ya'yansu.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 2 za su ba 'yan banga AK-47, rundunar soji ta yi martani mai zafi

Rundunar ‘yan sanda ta ce an sace dalibai 73 lokacin da 'yan bindiga suka mamaye makarantar da misalin karfe 11 na safiyar Laraba da ta gabata. Dalibai biyar, dukkansu 'yan mata, sun tsere daga hannun 'yan bindigan ranar Alhamis.

Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa, a ranar Juma’a, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci kamfanonin sadarwa da su katse sabis na sadarwa a Zamfara - lamarin da ya haifar da rashin sadarwar wayoyin salula a jihar.

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

A wani labarin, Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta umarci dukkan kamfanonin sadarwa da su katse hanyoyin sadarwarsu a jihar Zamfara, Daily Nigerian ta ruwaito.

A daya daga cikin wasikun da aka aike wa kamfanonin, mataimakin shugaban hukumar Umar Danbatta a ranar Juma'a 3 ga watan Satumba ya ce matakin na daya daga cikin dabarun da jami'an tsaro ke bi na dakile 'yan bindiga da ke addabar jihar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

A cewarsa:

“Matsalar tsaro a jihar Zamfara ta sanya dole a kkatse dukkan ayyukan sadarwa a jihar daga yau 03 ga Satumba, 2021.
"Wannan zai baiwa hukumomin tsaro da suka dace damar aiwatar da ayyukan da ake bukata don magance kalubalen tsaro a jihar, daidai da bukatun, an umarci Globacom da ta rufe dukkan shafuka a jihar Zamfara da kowane rukunin yanar gizo a cikin makwabciyar jihar da za ta iya bayar da sabis na sadarwa a jihar Zamfara.
“Rufe shafin na sati biyu ne (03 ga Satumba - 17, 2021) a matakin farko. Ana bukatar daukar matakin gaggawa a wannan batun.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel