Garin kai hari, 'yan sanda suka samu nasarar harbe shugaban 'yan bindiga a jihar Neja

Garin kai hari, 'yan sanda suka samu nasarar harbe shugaban 'yan bindiga a jihar Neja

  • Rundunar 'yan sanda a jihar Neja ta samu nasarar hallaka wani shugaban 'yan bindiga da yaransa
  • An ruwaito cewa, 'yan sanda tare da 'yan banga ne suka fatattaki wasu 'yan bindigan a wani dajin Neja
  • A halin yanzi an kwato babura da wasu manyan makamai daga hannun 'yan bindigan yayin da wasu suka tsere

Neja - Jami’an rundunar da ke yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Najeriya, tare da tallafin 'yan banga, a ranar Litinin 30 ga watan Agusta sun hallaka wani sanannen shugaban ‘yan bindiga, Jauro Daji, a jihar Neja.

Sun kuma kashe wasu 'yan bindiga da yawa yara ga Daji a yankin Kontagora na jihar.

An kuma kwato babura goma daga hannun 'yan bindigar.

A cewar majiyar, rundunar 'yan sandan ta yi aiki da sahihan bayanan sirri kuma ta yi wa 'yan bindigan kwanton bauna, inda suka kashe Daji, tare da yaransa, wadanda ke kokarin tsallaka wani rafi a cikin daji, don yin garkuwa da mutane a wani gari.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka ofishin ƴan sandan Zamfara, sunyi kisa, sun sace bindigu AK-47 masu yawa

Da yake zantawa da PRNigeria, daya daga cikin majiyoyin, wani jami’in leken asiri ya ce:

“Hadin gwiwar 'yan sanda da ‘yan banga na yankin ne suka kashe Jauro Daji tare da kashe 'yan bindigan dake shirin yin garkuwa da mutanen da basu ji ba basu gani ba a wani kauye.
“Shahararre Jauro Daji wanda ake zargin yana da hannu a hare-haren da aka kai kauyuka da makarantu ya jagoranci sauran 'yan bindigan masu yawa akan babura.
“An yi nasarar aiwatar da aikin a ranar Litinin tsakanin Gulbin Boka zuwa yankin Dogon Fadama a karkashin karamar hukumar Kontagora. Mun kuma kwato babura goma.
"Mun dauki kwararrun masu iyo domin gano makaman wasu daga cikin 'yan bindigan da suka tsere da gawawwakinsu da aka jefa cikin kogi."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun bindige Buba Baromi, kasurgumin mai kai wa 'yan bindiga bayanai a Niger

Rikici ya barke tsakanin Hausawa 'yan kasuwa da Fulani makiyaya a jihar Delta

Rikici ya barke a yankin Sapele, Karamar Hukumar Sapele ta jihar Delta yayin da ‘yan kasuwa Hausawa da Fulani makiyaya a yankin a ranar Litinin suka yi artabu da kare-jini-biri-jini a Kasuwar Hausa da ke kan hanyar Benin zuwa Warri, Amukpe, a cikin birni.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce akalla mutane goma ne suka samu munanan raunuka a cikin farmakin da ya biyo baya sannan aka garzaya da su asibitoci daban-daban a yankin, in ji rahoton Daily Report Nigeria.

Punch ta ruwaito cewa, an lalata shagunan katako, lamarin da ya haifar da cunkoson ababen hawa yayin da wasu masu ababen hawa suke tsere suka bar ababen hawansu domin tsira.

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wani labarin, Hukumomin karamar hukumar Jos ta Arewa, a ranar Lahadin da ta gabata, sun ce za su bibiyi duk wani mutumin da ya kai hari kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba kuma su kama su don fuskantar fushin doka, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Sun kuma ce za su cafke mazauna unguwar ko yankin da abin ya faru don tabbatar da abin da ya dace idan wadanda ake zargi suka tsere.

Wannan ci gaban na zuwa ne bayan harin da aka kai wa matafiya musulmai a ranar 14 ga watan Agusta a kusa da hanyar Gada-biyu-Rukuba na karamar hukumar Jos ta Arewa da kuma tashin hankalin da ya biyo baya a wasu yankuna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.