Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

  • A jihar Katsina, wasu 'yan bindiga sun mamaye gidan wani dan majalisa sun sace iyalansa
  • Rahoto ya bayyana cewa, an sace matar dan majalisar da kuma 'ya'yan biyu a daren jiya Asabar
  • Kafin wannan, 'yan bindiga sun taba sace dan majalisar, suka tsare shi har sai da aka biya fansa

Katsina - Wasu gungun 'yan bindiga sun mamaye garin Kurami, garinsu Ibrahim Aminu Kurami, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bakori a majalisar dokokin Katsina, inda suka sace matarsa da 'ya'yansa biyu, Daily Trust ta ruwaito.

Hakan na zuwa ne kusan shekara guda bayan da aka sace dan majalisar da kansa kuma aka tsare shi na tsawon kwanaki har sai da aka biya kudin fansa.

'Yan bindigar sun zo ne akan babura da motoci da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, inda suka tare hanyar Funtua zuwa Katsina na mintuna yayin da ake kokarin sace iyalan dan majalisar a gidansa, in ji wata majiya.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

'Yan bindiga sun yi awon gaba da iyalan dan majalisar dokoki a Katsina
'Yan bindiga | Hoto: daiulytrust.com
Asali: Twitter

Wata majiya da aka bayyana da Muhammad Kurami yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Nan da nan bayan sallar Ishaa’i muka fara jin harbe-harben bindiga a cikin garin, kafin mu ankara sun riga sun mamaye mahimman hanyoyin garin don gujewa duk wani yunkuri da mazauna yankin ka iya yi don dakile su.
"Sun tafi kai tsaye zuwa gidan mai martaba kuma sun tafi da matarsa da 'ya'yansa biyu."

Ya kara da cewa a yayin garkuwar, 'yan bindigar sun raunata wani Abdulhakim Ubaidu.

Mazauna garin da 'yan banga a yankin sun fara bin diddigin lamarin.

Wani babban jami'in tsaro, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa an tura jami'an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru da kuma majalisar a daren Asabar, in ji rahoton Punch.

Jami'in ya ce:

"Mutanen mu sun kasance a can (Kurami) tun daren Asabar kuma tuni aka fara gudanar da bincike don gano wadanda aka sacen su uku."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke dan bindigan da ya sace daliban Kwalejin Noma na Afaka

Ba a sami jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ba, yayin da layukan wayarsa basa shiga.

An sace wani attajiri da 'ya'yansa mata a makon da ya gabata

Kafin harin na jiya, a makon da ya gabata a daren 28 ga watan Agusta wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun mamaye garin Bakori kuma sun sace Alhaji Amu da 'ya'yansa mata biyu da kuma kanin Hakimin Bakori, Idris Sule Idris.

Har zuwa lokacin wannan rahoton wadanda abin ya rutsa da su na tare da masu garkuwa da mutanen.

Yankunan karamar hukumar Bakori, Funtua da Danja suna cikin yankunan da ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga a watannin baya.

'Yan ta'adda sun shafe shekaru da dama suna hargitsa garuruwan makwabta; Faskari, Kankara, Sabuwa da Dandume wanda ya haifar da gudun hijira daga mazauna kauyukan zuwa wasu yankuna.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

Kara karanta wannan

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

A wani labarin, 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.

Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar. Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba.

Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.