Dama Ta Samu: Gwamna Radda Ya Fadada Shirin Daukar Masu 'First Class' Aikin Gwammati

Dama Ta Samu: Gwamna Radda Ya Fadada Shirin Daukar Masu 'First Class' Aikin Gwammati

  • Gwamna Dikko Radda ya fadada tayin daukar aiki kai tsaye ga ɗaliban jihar Katsina da suka kammala digiri da sakamako mafi daraja (First Class)
  • Wannan mataki zao shafi dukkan ɗalibai 'yan asalin jihar Katsina da suka kammala karatu a jami’o’in Najeriya daga wannan shekara
  • Gwamna Radda ya ce hakan zai taimaka wajen gina ƙwararren ma’aikatan gwamnati a cikin shekaru 10 zuwa 15 masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya sanar da faɗaɗa tsarin ba wa ɗaliban jihar da suka kammala karatu da sakamakon digiri na farko (First Class) aiki kai tsaye.

Gwamna Radda ya bayyana hakan ne yayin bikin rufe Makon Daliban Jihar Katsina karo na farko da aka gudanar a Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).

Kara karanta wannan

'Yan takara 6 mafi yawan shekaru da za su fafata a zaben gwamnan Ekiti

Gwamn Radda.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda yana jagorantar taron Majalisar zartarwa Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Gwamna Radda ya fadada shirinsa

Vanguard ta rahoto cewa gwamnan ya ce an ƙirƙiro wannan tsari ne domin jawo ƙwararrun matasa cikin aikin gwamnati tare da ƙarfafa ingancin ayyukan ma’aikata a jihar Katsina.

“Lokacin da na hau mulki, na ƙaddamar da tsarin ba wa ɗaliban da suka kammala digiri da First Class aiki kai tsaye. Mun fara aiwatar da hakan a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da sauran manyan makarantu da ke Katsina.
“Yanzu na amince da faɗaɗa wannan dama ga dukkan ɗaliban Katsina da suka kammala da First Class a kowace jami’a a Najeriya daga wannan shekara zuwa gaba.”

Yadda tsarin zai amfani jihar Katsina

Dikko Radda ya bayyana cewa idan aka ɗauki adadi mai yawa na masu irin wannan sakamako aiki, jihar za ta zama ɗaya daga cikin mafi ƙwararrun ma’aikatan gwamnati a Najeriya nan da shekaru 10 zuwa 15.

A cewarsa, hakan zai sa ma’aikatan jihar Katsina su iya gogayya da takwarorinsu a sauran jihohi har ma da na gwamnatin tarayya, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Roko na musamman da Sarki Sanusi II ya yi ga kungiyar EU game da Kano

Gwamnatin Katsina ta tallafa wa ɗalibai

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen biyan basussukan tallafin karatu da kuma ƙara alawus-alawus na ɗalibai domin ƙarfafa su su ci gaba da neman ilimi.

Ya ce matakan da aka ɗauka sun taimaka wajen rage yawan yara marasa zuwa makaranta tare da hana matasa fadawa cikin ayyukan da ba su dace ba.

Radda.
Shugaban jami'ar BUK, Farfesa Haruna Musa-Muhammad tare da Gwamna Dikko Radda Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ilimi na gaba-gaba a gwamnatin Radda

Radda ya jaddada cewa ilimi na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta ba fifiko, inda ake ware kaso mai yawa na kasafin kuɗin jihar ga ɓangaren ilimi.

Ya ƙara da cewa gwamnati ta ɗauki malamai sama da 10,000 aiki tare da gina sababbin makarantu da gyaran kayayyakin more ilimi a faɗin jihar.

Gwamna Radda ya gana da sarakuna

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gana da sarakunan gargajiya kan matsalar rashin tsaro.

Ganawar ta fi mayar da hankali ne a kan muhimman batutuwan da suka shafi shugabanci, ci gaban al'umma, da kuma tsaro,

Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin sarakunan gargajiya wajen haɓaka zaman lafiya, tsaro, da kuma ci gaban al'ummomin mazauna karkara a faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262