'Yan Bindiga Sun Kaddamar da Sabon Hari Filato, Sun Hallaka fiye da Mutane 15
- 'Yan bindiga sun hallaka akalla mutane 19 a wani harin dare da suka kai kan wani kauye da cikin karamar hukumar Bokos, jihar Filato
- Wasu mazauna kauyen sun ce 'yan ta'adddar sun kai masu hari ne da misalin karfe 11:40 na dare tare da bude wuta kan mai uwa da wabi
- Shugaban matasan Bokkos wanda ya tabbatar da harin ya ce sun kwashe gawarwaki kusan 19 yayin da jami'an tsaro suka isa yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Filato - Akalla mutane 19 sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani harin da ‘yan bindiga suka kai Filato.
An ce 'yan bindigar sun farmaki kauyen Kawel da ke gundumar Mushere, karamar hukumar Bokkos a daren ranasr Lahadi yayin da jama’a ke barci.

Source: Facebook
'Yan bindiga sun kai hari Filato
Wani mazaunin yankin, Malo Bitrus, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa maharan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 11:40 na dare.
Malo Bitrus ya shaidawa jaridar cewa, maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi a cikin kauyen, lamarin da ya jefa mazauna garin cikin tsananin firgici.
Ya kara da cewa da yawa daga cikin mazauna kauyen sun tsere zuwa cikin dazuzzuka a lokacin da suke jiwo karar harbe harbe, yayin da harin ya rutsa da wasu.
Yadda harin ya kasance a kauyen Kawel
A cewar rahoton, harin ya faru ne a Kauyen Kawel da ke gundumar Mushere, inda ‘yan bindigar suka yi wa garin kawayenya tare da afkawa gidaje.
Mazauna garin sun ce maharan sun yi ta yi harbi ta ko’ina, lamarin da ya jawo mutuwar mutane 19 da kuma jikkatar wasu da dama.
Wani shugaban matasa na karamar hukumar Bokkos, Christopher Luka, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun samun labarin harin tun da tsakiyar dare.
Ya ce bayan samun rahoton, ya hanzarta yin kiran gaggawa ga jami’an tsaro da ke yankin domin su kai dauki.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Ɗan kasuwa ya mutu a wani yanayi a ɗakin fitacciyar 'yar TikTok a jihar Kano

Source: Original
Jami'an tsaro sun kai dauki
Luka ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun tabbatar da mutuwar mutane 19, yayin da ake ci gaba da tantance cikakken barnar da aka yi a yankin.
Ya kuma ce jami’an tsaro sun fara kai dauki da kuma tabbatar da tsaro a kauyen da abin ya shafa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Ya bayyana harin a matsayin abin takaici, inda ya bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su kara kaimi wajen kare rayukan jama’a a yankin.
An kashe mutane a harin Filato
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu miyagun 'yan bindiga sun farmaki yankin Angwan Rukuba dake ƙaramar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
Shaidun gani da ido sun ce 'yan ta'addan sun farmaki Rukuba ne a daren ranar Lahadi, 29 ga Maris, 2026, inda suka kashe mutane masu yawa.
Biyo bayan wannan hari, wasu fusatattun matasa a yankin sun toshe manyan hanyoyi, inda rahotanni suka nuna cewa an kashe wasu masu Keke Napep da fasinjojinsu a matsayin ramuwar gayya.
Asali: Legit.ng
