Rahoton Fasaha: Ɓarayi Sun Sace Dalibai 1,409 a Najeriya Cikin Watanni 19, Miliyoyi Sun Salwanta Wajen Fansa

Rahoton Fasaha: Ɓarayi Sun Sace Dalibai 1,409 a Najeriya Cikin Watanni 19, Miliyoyi Sun Salwanta Wajen Fansa

  • Wani rahoto ya bayyana cewa aƙalla dalibai 1,409 mahara suka sace daga makaranta cikin watanni 19 a Najeriya
  • Rahoton wanda wata ƙungiyar fasaha SBM ta fitar ya nuna cewa ɗalibai 16 daga ciki sun rasa rayuwarsu
  • Harin baya-bayannan da ɓarayi suka sace ɗalibai shine wanda ya faru a jihar Zamfara

Abuja - Wani sabon rahoto da ƙungiyar fasaha ta SBM ta fitar ya nuna cewa aƙalla ɗalibai 1,409 aka sace a faɗin Najeriya cikin watanni 19 da suka shuɗe.

Rahoton wanda akai wa take, "Sace ɗalibai daga makarantu a Najeriya," kungiyar ta bayyana adadin waɗanda hare-haren suka shafa tun daga watan Maris, 2020, zuwa yanzu.

The Cable ta ruwaito cewa yan bindiga sun sace ɗalibai 1,119 daga makarantunsu daga shekarar 2014 zuwa 2020.

Kara karanta wannan

Bayan Datse Sabis a Zamfara, Gwamnatin Tarayya Ta Yi Magana Kan Datse Sabis Na Sadarwa a Jihar Katsina

Rahoton fasaha kan sace ɗalibai a Najeriya
Rahoton Fasaha: Ɓarayi Sun Sace Dalibai 1,409 a Najeriya Cikin Watanni 19, Miliyoyi Sun Salwanta Wajen Fansa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wani rahoto na daban da aka buga ya nuna cewa dalibai 821 ne harin yan bindiga ya rutsa da su a watanni 9 na shekarar 2021.

Adaɗin da ya zarce kashi biyu cikin uku na daliban da aka sace a Najeriya cikin shekara bakwai da suka gabata.

Bugu da ƙari a rahoton kwanan nan da ƙungiyar fasaha ta SBM ta fitar, tace ɗalibai 1,409 ne lamarin ɓarayin ya shafa tun sanda lamarin ya dawo ɗanye a watan Maris, 2020, inda 16 daga cikinsu suka mutu sanadiyyar haka.

Waɗanne jihohi lamarin yafi kamari?

Rahoton ya kuma bayyana cewa cewa jihar Katsina ce kan gaba inda aka sace ɗalibai 440, jihar Zamfara ke take mata baya da 419 yayin da jihohin Kaduna, Neja da Kebbi suka cike ragowar.

Kara karanta wannan

Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara

Wani sashin rahoton yace:

"Aƙalla ɗalibai 1,409 ɓarayi suka sace tun daga sanda lamarin ya sake dawowa ɗanye, wanda ya soma a watan Maris 2020."
"A hare-hare 19 har zuwa na baya-bayannan da aka yi a Zamfara, an yi garkuwa da malamai 17 tare da ɗalibansu. Kuma aƙalla miliyan N220m aka biya a matsayin kuɗin fansa."
"Abu mara daɗi shine ɗalibai 16 daga cikin waɗanda lamarin ya shafa a tsawon wannan lokacin sun rasa rayuwarsu sanadiyyar lamarin."

A wani labarin kuma Zaka Zubar da Mutuncinka a Idon Yan Najeriya Matukar Ka Sauya Sheka Zuwa APC, Jigon PDP Ya Faɗawa Jonathan

Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Dr Okwesilieze Nwodo, ya gargaɗi tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan kada yayi gangancin komawa jam'iyya mai mulki APC, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Nwodo ya bayyana cewa matukar Jonathan ya koma APC to ya zubar da ragowar mutuncinsa da kimarsa a idon yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Barayin da Suka Sace 'Ya'ya da Matar Babban Malamin Addini Sun Nemi a Tattaro Musu Miliyan N50m

Asali: Legit.ng

Online view pixel