Sabon hari: 'Yan bindiga sun sace wani sarkin gargajiya a jihar Neja
- Wasu 'yan bindiga sun dira gidan sarkin gargajiya a garin New Bussa, hedkwatar karamar hukumar Borgu
- Rahotanni sun bayyana cewa, an sace sarkin ba tare da an raunata kowa a fadar sarkin ba
- Rundunar 'yan sanda a jihar ta Neja ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma yi martani kan sace sarkin
Neja - 'Yan bindiga sun sace Mahmud Aliyu, Dodo na Wawa, sarkin gargajiya a garin New Bussa, hedkwatar karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Rahotanni sun ce an sace basaraken ne daga fadarsa a ranar Asabar.
Wasiu Abiodun, mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar Neja, ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar TheCable ranar Lahadi 5 ga watan Satumba.
Abiodun ya ce an tura jami’an tsaro don bin diddigin 'yan bindigan tare da ceto wanda aka sace.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A jawabansa kan martanin hukuma, Abiodun ya ce:
"An tura tawagar 'yan sanda da 'yan banga na yankin domin farautar 'yan bindigar don ceto wadanda abin ya shafa tare da cafke masu laifin.
Ta yaya suka sace sarkin?
'Yan bindigar, wadanda adadinsu ya kai kusan 20, an ce sun mamaye fadar ne suna ta harbe-harbe, inji rahoton The Nation.
Bayanai sun ce basaraken ya buya a dakinsa kafin 'yan bindigan su dauke shi da karfi.
An ce an tafi da shi shi ba tare da 'yan bindigar sun cutar da kowa a fadar ba.
A cewar wani shaidan gani da ido:
”Sun zo a kan babura da misalin karfe 10 na daren jiya suna harbin iska wanda ya jefa gaba dayan fadar da yankin cikin firgici.
"Sun tafi tare da sarkinmu kuma a halin yanzu, ba a ji komai ba game da inda yake"
Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina
A wani labarin, wasu gungun 'yan bindiga sun mamaye garin Kurami, garinsu Ibrahim Aminu Kurami, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bakori a majalisar dokokin Katsina, inda suka sace matarsa da 'ya'yansa biyu, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne kusan shekara guda bayan da aka sace dan majalisar da kansa kuma aka tsare shi na tsawon kwanaki har sai da aka biya kudin fansa.
'Yan bindigar sun zo ne akan babura da motoci da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, inda suka tare hanyar Funtua zuwa Katsina na mintuna yayin da ake kokarin sace iyalan dan majalisar a gidansa, in ji wata majiya.
Asali: Legit.ng