Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

  • Babban malamin addinin Islama, Sheikh Muhammad Khalid ya koka kan mulkin shugaba Buhari
  • Ya bayyana cewa, wannan gwamnati ta Buhari ba ta tsinana komai ba duk da irin addu'o'in da ake mata
  • Ya kuma bayyana cewa, yawaitar kisa a kasar yana daukar salon kisan kare dangi irin na kasar Rwanda

Abuja - Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.

A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.

A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.

Kara karanta wannan

Buhari yace yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yana da matukar wahala

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid
Sheikh Muhammad Khalid | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A bangare guda, ya kuma bayyana cewa, addininsa ya horar da shi da fadin gaskiya da adalci, don haka dole ne ya fadi gaskiya game yadda mulkin Buhari yake kamar yadda ya yi a lokacin Jonathan.

Abubuwa a fili sun nuna Buhari ya gaza

Da wakilin jaridar Punch ya tambaye shi shin yana da wata matsala da gwamnatin Buhari ganin yadda ya caccaki shugaban a wani bidiyo? malamin ya amsa da cewa:

"Halin kasar ya sanar da haka, kuma ina kan hanya madaidaiciya domin addinina ya horar da ni da yin adalci kuma dole na yi.
"Idan na fadi irin wadannan abubuwa a lokacin (Goodluck) Jonathan amma ba na son in fade su yanzu saboda ina addini na daya da Shugaban kasa, to ni munafuki ne.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

"Abinda na dauka shine dukkan mu 'yan Najeriya ne kuma mun cancanci mu zauna lafiya.
"Na yi imani dole ne a yi abubuwa da yawa a cikin wannan kasar kuma dole ne a yi su cikin sauri.

Kisan kare dangi ake a Najeriya

Da yake kokawa kan yadda kashe-kashe ke kara yawa a kasar, malamin ya bayyana cewa, halin da ake ciki ya yi kama da shirin kisan kare dangi irin wanda ya faru a kasar Rwanda.

Hakazalika, malamin ya ce an fi kashe mutane da yawa a wannan mulkin na Buhari fiye da mulkin Jonathan, lokacin da shugaba Buhari ya yi alkawarin dawo da zaman lafiya a kasar.

A cewarsa:

"Na je Rwanda na ga abin da ya faru a can. A Najeriya, hakika muna wasa da wuta.
"Kashe-kashen da ake yi a kasar na daukar salon kisan kare dangi kuma shi ya sa mutane ke mutuwa a kullum.

Kara karanta wannan

Jerin manyan jami'an gwamnati 5 da shugaba Buhari ya kora cikin kankanin lokaci

"Ana kashe mutane da yawa a wannan mulkin fiye da na gwamnatin da ta gabata.
"Ku yi binciken ku kuma kwatanta shi tare da adadin mutanen da aka kashe a cikin gwamnatin da ta gabata."

Mun yi ta addu'a ba mu ga sakamako ba

Da aka tambaye shi shin a matsayinsa na malami ba addu'a ya kamata ya yi ba malamin ya amsa da cewa:

"Gaskiyar ita ce ba za mu iya musanya ayyuka da addu'o'i ba. Amma yi masa addu’a ya yi me? Zan yi masa addu’a ne don ya dauki mataki, ba wai ya yi watsi da nauyin da ke kansa ba.
"Addu'a ba ta aiki a haka kuma shi ya sa na ce idan yana da burin cika alkawuransa, Allah ya taimake shi. Baya ga haka, mun jima muna yi masa addu’a, menene sakamakon?

Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar cafke mutanen da ke da hannu a kashe-kashen da aka yi a jihar Filato, inji rahoton TheCable.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

A cikin watanni uku da suka gabata, hare-hare a sassa daban-daban na jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.

Buhari, wanda Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya wakilta, a wani zaman tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki a jihar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, ya bukaci tattaunawa mai dorewa don samar da zaman lafiya a Filato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.