Mazauna a Sokoto sun hallaka 'yan ta'adda 6, sun kone gawarwakinsu kurmus
- 'Yan ta'adda sun gamu da ajalisu bayan da suka hallaka wasu mutane biyu da suka sace a Sokoto
- Rahoto ya bayyana cewa, 'yan bindigan sun ki karbar kudin fansa bayan sace wasu mutane biyu
- Mazauna gari sun yi wa 'yan bindigan dirar mikiya, inda suka hallaka su suka kone gawarwakinsu
Sokoto - Akalla 'yan ta'adda shida, wadanda aka fi sani da 'yan fashin daji, mazauna kauye suka kashe a garin Tangaza na jihar Sokoto, Daily Nigerian ta ruwaito.
An rahoto cewa 'yan ta'addan sun sace mutane biyu a garin tare da yin watsi da tayin kudin fansa a makon da ya gabata.
Bayanai sun ce, duk da haka, 'yan ta'addan sun dage kan cewa sai sun kashe wadanda suka sacen don daukar fansa kan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa a maboyarsu, kuma sun yi hakan.
Cikin fushi da kisan mutanen biyu da aka sace, wasu mazauna garin da 'yan banga suka shiga dazuzzukan ne don neman 'yan ta'addan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin garin da ya zanta da BBC Hausa da ya nemi a sakaya sunansa ya ce 'yan banga sun bibiyi maharan guda shida a maboyarsu, inda suka cafke su suka mika su ga 'yan sanda.
A cewarsa:
“Dubunnan mazauna garin suka yi tururuwa suka nace a ba su 'yan ta’addan su kashe su.
“Lokacin da 'yan banga suka kai su ofishin ‘yan sanda, mutanen sun yi kokarin kona ofishin 'yan sandan. ‘Yan sanda suka koresu."
A cewarsa, bayan haka sai gungun mutanen suka yi wa ‘yan ta’addan dirar mikiya tare da kona gawarwakin su.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Sunusi Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Janar Faruk Yahaya: Za mu ji da 'yan bindiga da yaren da suke fahimta
Babban Hafsan Sojoji (COAS), Laftanal Janar Faruk Yahaya, ya ce za a bi da ‘yan bindiga, masu tayar da kayar baya da masu garkuwa da mutane “cikin yaren da suke fahimta.”
Ya bayyana hakan ne a jiya Laraba 15 ga watan Satumba yayin bikin rufe wani taro da babban hafsan sojan ya hada kashi na biyu da na uku a Abuja, Premium Times ta ruwaito.
Kalaman shugaban sojojin sun fito ne a yayin da ake samun karuwar hare-hare daga ‘yan bindiga a fadin kasar, wanda ke haddasa kashe-kashe da sace mutane.
Yahaya ya ce sojoji na ci gaba da jajircewa kan aikinsu na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.
An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa
A baya kin ji cewa, Ma’aikata bakwai na Ma’aikatan Kiwon Lafiya na Kananan Hukumomin Kwami da Billiri a Jihar Gombe a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda saboda karkatar da 5,450 gidajen sauro masu magani (ITNs) da ake rabawa kyauta a al'ummomin su.
Gwamnatin jihar, tare da tallafi daga Asusun Duniya, Catholic Relief Serive da Shirin kawar da zazzabin cizon sauro sune masu tallafawa wajen rarraba gidajen sauron kyauta, Daily Trust ta ruwaito.
Kwamishinan lafiya a jihar Gombe, Dr Habu Dahiru, ya fadawa wani taron manema labarai a Gombe ranar Asabar cewa an cafke wadanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng