Barayin da Suka Sace 'Ya'ya da Matar Babban Malamin Addini Sun Nemi a Tattaro Musu Miliyan N50

Barayin da Suka Sace 'Ya'ya da Matar Babban Malamin Addini Sun Nemi a Tattaro Musu Miliyan N50

  • Barayin da suka jagoranci sace matar wani babban malamin addinin kirista a Abuja da ƴaƴansa mata biyu sun nemi fansa
  • Wata majiya tace maharan sun kira ɗaya daga cikin makusantan waɗanda aka sace ranar Lahadi da karfe 11:00 na dare
  • Da farko ɓarayin sun nemi a biya miliyan N100m kuɗin fansa, amma daga bisani suk sakko zuwa miliyan N50m

Abuja - Yan bindigan da suka sace iyalan Fasto a Abuja, matarsa da ƴaƴansa mata biyu sun nemi a tattaro musu miliyan N50m kuɗin fansa.

Dailytrust ta ruwaito cewa maharan sun farmaki gidan babban malamin dake Zone A, yankin Pegi, karamar hukumar Kuje, ranar Lahadi.

Yayin harin ne ɓarayin suka yi awon gaba da matarsa da yayan sa mata guda biyu, Glory Oladapo da Moyo Oladapo.

Barayi sun nemi kuɗin fansa
Barayin da Suka Sace 'Ya'ya da Matar Babban Malamin Addini Sun Nemi a Tattaro Musu Miliyan N50 Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa Fasto Oladapo, wanda malamin cocin RCCG ne dake Pegi, ya yi tafiya zuwa wani gari lokacin da lamarin ya faru.

Kara karanta wannan

Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaushe ɓarayin suka kira iyalan malamin?

Wata majiya cikin iyalan faston, wanda ya nemi a sakaya sunan shi, yace maharan sun gabatar da bukatarsu ranar Lahadi da daddare.

Yace ɓarayin sun kira ɗaya daga cikin iyalan waɗanda suka sace, inda suka bukaci a haɗa musu miliyan N100 kuɗin fansa da farko.

Yace:

"Sun kira waya ranar Lahadi da daddare da misalin karfe 11:00 kuma wanda suka kira ya yi magana da matar faston da yaran biyu."
"Da farko ɓarayin sun nemi tsabar kuɗi miliyan N100m amma daga baya suka sakko zuwa miliyan N50m."

Mutumin ya kara da cewa a halin yanzun an cigaba da tattaunawa da ɓarayin domin su rage makudan kuɗin da suka sanya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Duk wani kokari na jin ta bakin kakakin rundunar yan sandan Abuja, ASP Daniel Y Ndiparya, ya ci tura kuma bai daga kiran waya ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afka wa wani gari a Niger, sun sace kaya a shaguna da kuɗaɗen mutane

A wani labarin kuna kun ji cewa Bayan Datse Sabis, Jiragen Yakin Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Kan Sansanonin Yan Bindiga a Zamfara

Kwanaki ƙalilan bayan gwamnatin Zamfara ta sanar da ɗaukar wasu matakai domin magance ayyukan yan bindiga, sojojin sama da na ƙasa sun yi luguden wuta kan yan bindiga a sansanonin su.

Jiragen yakin sama na sojoji ne suka fara ruwan wuta kan yan tada kayar bayan daga bisani sojin ƙasa suka buɗe wuta kan masu tserewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel