'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu

  • A wani sabon harin 'yan bindiga, an hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu a Kaduna
  • Sojoji sun kuma ceto wasu mutane uku matafiya a wata hanyar a Kaduna bayan an sace su
  • Gwamna El-Rufai ya yi Allah wadai da harin, ya kuma yi addu'ar Allah ya jikan mamatan

'Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a kauyen Makoro Iri dake karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A cewar wani rahoton tsaro, 'yan bindigar sun mamaye kauyen inda suka harbe mutane biyu da aka bayyana sunayensu da Gideon Mumini da Barnabas Ezra, Daily Trust ta ruwaito.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi 29 ga watan Agusta.

'Yan bindiga sun mamaye wani kauye a Kaduna, sun hallaka mutane biyu
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai | Hoto: dailytrust.com

Sojoji sun ceto matafiyan da aka sace

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wani labarin kuma, rundunar Operation Safe Haven ta ceto matafiya uku daga hannun 'yan bindiga a hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo a karamar hukumar Jema’a.

'Yan bindigan da suka tare hanya sun sace matafiya.

Sojoji sun amsa kiran gaggawa sannan sun bi 'yan bindigan, inda suka kubutar da matafiya uku.

An kuma gano motar matafiya da aka ceto kirar Peugeot 307.

Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna bacin ransa game da rahoton harin da aka kai kauyen Makoro Iri na karamar hukumar Kajuru, ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka mutu, yayin da ya aika da ta’aziyya ga iyalansu.

Doka a Zamfara: Gwamna ya ba da umarnin a harbe masu goyon biyu a babur

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ba da umarnin rufe dukkan kasuwannin mako-mako a jihar a matsayin wani mataki na magance matsalar tabarbarewar tsaro a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ba da rahoton cewa gwamna Matawalle ya sanar da hakan ne bayan ya karbi dalibai 18 da aka yi garkuwa da su a Kwalejin Aikin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar dake garin Bakura.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatin jihar ta hana sayar da man fetur a cikin jarkoki a wani mataki na dakile samar da man ga 'yan bindiga, hakazalika da kuma ba da umarnin harbin masu babur dake goyon biyu.

Bayan shafe kwanaki 88, 'yan bindiga sun sako daliban Islamiyyar Tegina da suka sace

A wani labarin, Sama da dalibai 70 'yan bindiaga suka sako na makarantar Islamiyya da ke garin Tegina wadanda aka yi garkuwa da su kwanaki 88 da suka gabata, PR Nigeria ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun bayyana cewa, an sace daliban ne a harabar makarantar Islamiyyar dake Tegina a watan Yunin 2021.

Wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar PRNigeria cewa daliban na kan hanyarsu ta zuwa Minna akan hanyar Kagara daga Birnin Gwari.

An tsare daliban Islamiyyar na tsawon kwanaki 88 da awanni 11 gwargwadon lokacin da suka shafe a hannun 'yan bindigan kenan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel