'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

  • Wasu 'yan bindiga sun tare motar wani jigon PDP, inda suka yi awon gaba dashi tare da direbansa
  • Rahotanni sun bayyana cewa, jigon na PDP yana kan hanyarsa ta zuwa gona ne lokacin da lamarin ya faru
  • Har zuwa lokacin hada wannan rahoto 'yan sanda basu tabbatar da faruwar lamarin ba, amma danginsa sun sanar da hakan

Edo - Rahotanni sun bayyana cewa an sace wani jigon jam’iyyar PDP kuma jagoran jam’iyyar a gundumar Sanatan Edo ta Kudu, Owere Dickson Imasogie tare da direban sa a safiyar yau.

An sace jigon ne a kan hanyarsa ta zuwa gonarsa lokacin da wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kama shi da misalin karfe 7 na safe, The Sun ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Da Duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da jigon PDP a jihar Edo
'Yan bindiga dauke da makamai | Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Wata majiya kusa da danginsa ta ce:

“An yi garkuwa da shi a gonarsa da ke kewayen yankin Obada a karamar hukumar Uhunmwonde. Yana tare da direbansa lokacin da lamarin ya faru."

A lokacin shigar da wannan rahoto, rundunar ‘yan sanda ba ta tabbatar ko ta yi wani bayani kan lamarin ba amma wata kungiya, Edo State Decide Movement, a cikin wata sanarwa, ta yi kira ga gwamnan jihar, Godwin Obaseki da ya ceto Owere Dickson.

A wani bangare na sanarwar, kungiyar ta ce:

“Cikin gaggawa, muna kira ga gwamnatin jihar ta Godwin Obaseki da ta dauki kwakkwaran mataki na ceto uba ga kowa da kowa daga hannun 'yan bindiga ko masu garkuwa da mutane wadanda makiyan ci gaba ne a jihar mu mai kaunar ci gaba."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

'Yan bindiga sun hallaka fasto a Kaduna, El-Rufai ya yi martani mai zafi

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe wani faston cocin Evangelical Church Winning All, Rev. Silas Ali, a karamar hukumar Zangon-Kataf ta jihar Kaduna.

Jaridar Punch ta samu labarin cewa 'yan bindigan su yi wa faston dirar mikiya a ranar Asabar 12 ga watan Satumba.

Kwamishinan tsaro na cikin gida da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Ya ce gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufai ya ji ba dadi kan harin sannan ya jajantawa cocin da dangin faston da aka kashe.

'Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina

A wani labarin, 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar.

Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba. Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel