'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

'Yan bindiga sun sace dalilan jami'a kwanaki kadan bayan sace malamansu

  • Wasu 'yan bindiga sun sace daliban jami'ar ABSU ta jihar Abia a hanyar zuwa makarantar
  • Rahoto a bayyana cewa, an sace daliban 10 tare da wasu mutane da ba a san adadinsu ba
  • Wata majiyar tsaro ta ce, an samu motoci uku a wurin da aka sace daliban, lamarin yake nuni da cewa akwai wasu daban da aka sace

Abia - Wasu 'yan bindiga sun sace dalibai 10 na Jami'ar Jihar Abia, Uturu (ABSU) a hanyar Ihube zuwa ABSU, Daily Sun ta ruwaito.

Sace daliban na zuwa ne makonni bayan da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da malaman jami’ar uku a kan hanyar Uturu/Isuikwuato.

Lamarin wanda rahotanni suka ce ya faru tsakanin karfe 5 na yamma zuwa 6 na yamma a ranar Asabar, ya jefa al’ummar jami’ar cikin rudani.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sace dalilan jami'ar Abia bayan sace malamansu
Jami'ar Abia | Hoto: sunnewsonline.com

An ba da rahoton cewa motar bas ta jihar Abia da ke jigilar fasinjoji zuwa makarantar, SUV da mota kirar Hilux mallakar wani kamfani an same su babu kowa a ciki a wurin da lamarin ya faru, abin da ke nuni da cewa ba daliban kadai aka sace ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiyar tsaro ta ce kawo yanzu ba a san adadin mutanen da aka sace ba.

Mazauna a Sokoto sun hallaka 'yan ta'adda 6, sun kone gawarwakinsu kurmus

Akalla 'yan ta'adda shida, wadanda aka fi sani da 'yan fashin daji, mazauna kauye suka kashe a garin Tangaza na jihar Sokoto, Daily Nigerian ta ruwaito.

An rahoto cewa 'yan ta'addan sun sace mutane biyu a garin tare da yin watsi da tayin kudin fansa a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun banka wuta gidan Kakakin majalisar wakilan jihar Zamfara

Bayanai sun ce, duk da haka, 'yan ta'addan sun dage kan cewa sai sun kashe wadanda suka sacen don daukar fansa kan hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa a maboyarsu, kuma sun yi hakan.

Cikin fushi da kisan mutanen biyu da aka sace, wasu mazauna garin da 'yan banga suka shiga dazuzzukan ne don neman 'yan ta'addan.

An yi ram da wasu ma'aikatan asibiti a Gombe da laifin sace gidan sauron talakawa

A wani labarin, Ma’aikata bakwai na Ma’aikatan Kiwon Lafiya na Kananan Hukumomin Kwami da Billiri a Jihar Gombe a halin yanzu suna hannun ‘yan sanda saboda karkatar da 5,450 gidajen sauro masu magani (ITNs) da ake rabawa kyauta a al'ummomin su.

Gwamnatin jihar, tare da tallafi daga Asusun Duniya, Catholic Relief Serive da Shirin kawar da zazzabin cizon sauro sune masu tallafawa wajen rarraba gidajen sauron kyauta, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Kwamishinan lafiya a jihar Gombe, Dr Habu Dahiru, ya fadawa wani taron manema labarai a Gombe ranar Asabar cewa an cafke wadanda ake zargin ne a ranar 10 ga watan Satumba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.