Sojoji Sun Bindige 'Yan Bindiga Tare da Kama Wasu a Kaduna

Sojoji Sun Bindige 'Yan Bindiga Tare da Kama Wasu a Kaduna

  • Sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe wasu mutane biyu da ake zargi 'yan bindiga ne yayin wata arangama da suka yi a Jihar Kaduna
  • Bayan fa haka, dakarun Najeriya sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi 'yan bindiga ne da ke kara ta'azzara matsalar tsaro a Najeriya
  • Dakarun kasar sun ƙwato dabbobin da 'yan ta'addan suka sace, makamai, harsasai, babura da na'urorin lantarki da suke amfani da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Dakarun Najeriya karkashin Operation Fansan Yamma (OPFY) sun kashe wasu mutane biyu da ake zargin 'yan bindiga ne a jihar Kaduna.

Sun kama wasu huɗu tare da ƙwato dabbobin da aka sace a jerin hare-haren hadin gwiwa da suka gudanar a faɗin jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da bam ya tarwatse da sojoji a Sokoto, an rasa rayuka

'Yan bindigan da aka kama a Kaduna
Mutum biyu da aka kama da zargin zama 'yan bindiga a Kaduna. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanai game da faramakin da dakarun Najeriya suka kai ne a wani sako da rundunar sojin kasar ta wallafa a shafinta na X.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga

Ayyukan da aka gudanar tsakanin ranakun 20 zuwa 21 ga watan Yunin 2026 sun kai ga ƙwato makamai, harsasai, babura da na'urorin lantarki da hukumomin soji suka ce suna ɗauke da hujjojin da ke alaƙanta waɗanda aka kama da ayyukan 'yan bindiga da ta'addanci.

A cewar rundunar sojin, an fara aikin ne a ranar 20 ga Yuni bayan samun sahihan bayanan sirri kan satar shanu a wani yanki da ke jihar Kaduna.

Dakarun sun yi gaggawar kai ɗauki tare da tsare waɗanda ake zargin yayin da suke ƙoƙarin tserewa, lamarin da ya haifar da musayar wuta inda aka kashe 'yan bindiga biyu da ake zargi.

Sojoji sun kwato shanu a Kaduna

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito

Jami'an tsaron da suka kai farmakin sun kuma ƙwato dabbobin da aka sace, makamai da harsasai, tare da dakile shirin aikata laifin.

Sai dai, hukumomin soji sun bayyana cewa farar hula guda ɗaya ya rasa ransa a yayin wannan lamari sakamakon abin da suka ce ya samo asali daga ayyukan 'yan bindigar.

Sojoji sun kama 'yan bindiga

A wani aiki daban da aka gudanar a wannan rana, dakarun da ke sintiri da daddare sun kama wasu mutane biyu da ake zargin 'yan bindiga ne.

Binciken da aka gudanar a kansu ya gano wasu bayanai da ke cikin na'urorin lantarki da ke alaƙanta su da ayyukan ta'addanci da 'yan bindiga a yankin.

Dan bindigan da aka kama
Daya daga cikin wadanda aka kama a Kaduna. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an tsare waɗanda ake zargin kuma ana ci gaba da gudanar da bincike a kansu a halin yanzu.

A ranar 21 ga Yuni, dakarun sun ci gaba da farmaki inda suka yi karo da wasu masu ɗauke da makamai, waɗanda suka tsere zuwa cikin daji sakamakon matsin lambar da sojoji suka yi masu.

Sojojin sun bi sawunsu, inda daga bisani suka kama wasu mutane biyu da ake zargin masu leƙen asirin 'yan bindiga ne, waɗanda ake zargin suna ba ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka bayanan sirri.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Neja, an kashe mutane da kona gidaje

Bello Turji ya fito da sabon bidiyo

A wani labarin, mun kawo muku cewa kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji ya fito a wani sabon bidiyo yana barazanar cigaba da kai hare-hare.

Dan ta'addan ya bayyana cewa a shirye yake ya cigaba da yaki da gwamnatin Najeriya idan ta ga za ta cigaba da amfani da karfin soja a kan shi da sauran mabiyansa.

A bayanin da ya yi, Bello Turji ya kara da cewa ya ba Najeriya zabin ko ta yi sulhu da shi ko kuma ta su cigaba da yaki da juna ba tare da ya mika wuya ga hukuma ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng