Sheikh Gumi: Da yawan shanun da ake sacewa a Arewa 'yan Kudu ake sayarwa

Sheikh Gumi: Da yawan shanun da ake sacewa a Arewa 'yan Kudu ake sayarwa

  • Sheikh Ahmad Gumi, ya sake jaddada cewa, ba laifin 'yan bindiga ne yadda suke aikata barna
  • Ya ce, mafi yawan shanun da ake sacewa daga yankin Arewa ana kasuwancinsu ne a kudanci
  • A cewarsa, jigilar shanun da ake sacewa shi ya kara tura kasar nan cikin matsalar da ta ke ciki

Kaduna - Malamin addinin Islama, Ahmad Gumi, ya bayyana cewa mafi yawan shanun da aka sace a jihar Zamfara da wasu jihohin Arewa maso yammacin kasar ana jigilar su zuwa kudancin kasar ne - kudu maso gabas, kudu maso kudu da kudu maso yamma a matsayin abinci.

Ya yi wannan fallasa mai ban al'ajabi ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin sa na Facebook ranar Litinin, 6 ga Satumba.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

A cewarsa, wannan satar ta taimaka wajen kara ta'azzarar matsalar 'yan bindiga da ake fuskanta a kasar a yau ba kadan ba.

Sheikh Gumi: Da yawan shanun da ake sacewa a Arewa 'yan Kudu ake sayarwa
Dr Ahmad Abubakar Gumi | Hoto: prnigeria.com
Asali: Facebook

Gumi yace:

"Daga cikin halin da ake ciki, a shekarar 2009 satar shanu ya zama ruwan dare. Yawancin shanun da aka sace sun nufi kudu dasu a cikin tirela inda ake siyarwa ana yanka su.
"Wannan babban jigila na satar shanu ya rage yawan samar dasu. Mafi yawan satar da farko ya shafi makiyaya na karkara kuma ya zama mafi yawa a yankin Arewa maso yamma."

Lokaci ya yi da ya kamata a kame Gumi

A bangare guda, mutane da yawa a kafar Facebook sun yi martani kan maganganun malamin, inda kowa ya bayyana ra'ayinsa kan malamin.

Ibrahim Hussaini, wani ya da yayi martani ya ce:

Kara karanta wannan

Shekaru 35 yana aikin koyarwa a Borno, dan Najeriyan da Turawa suka horar ya koma talla

“Duba da ra’ayin ka, ya kamata dukkan mu mu dauki makamai akan kasar tunda duk mun fuskanci wani rashin adalci ta wata hanyar.
"Na yi mamakin irin goyon bayan da ka ke ba wa wadannan 'yan ta'adda. Allah ya tona asirin ka da wadanda kake wakilta .. Allah zai kunyata ku duka !!! Lokaci ya yi da ya kamata a kama ka kuma babu abin da zai faru."

Ubaidu Yakubu ya ce:

"A ko yaushe ina tunanin yadda Mallam ke ba da bayani kan ayyukan 'yan bindiga, yadda yake watsi da muguntar da suke yi wa mutane bai dace da malami mai matsayinsa ba.
"Bai taba yin Allah wadai da kisan gillar da suka yi ba, yana ma jin suna fuskantar barazana daga gwamnati ne ta hanyar mayar da su saniyar ware wanda ba gaskiya bane. Ina matukar jin takaicin gamsuwa da tausayin da ya ke nuna masu."

Abubakar Abu Humaida ya ce:

Kara karanta wannan

'Yan banga sun bindige mai garkuwa da mutane yayin da ya je karbar kudin fansa

"Gwamnatocin Katsina da Zamfara sun yi ta tattaunawa inda aka kashe miliyoyin Nairori don gamsar da 'yan ta'adda amma abin takaici shine hakan ya kawai karfafa 'yan ta'adda ne, ya ba su karin lokaci da albarkatu don tara makamai sannan a karshe su ci gaba da barnarsu a karkashin rigar afuwa. Gwamnatin wauta ce kadai za ta tsaya kan abin da ake kira tattaunawa lokacin da ake kashe mutane da yawa a kullum.”

Sheikh Gumi: Tura sojoji su ragargaji 'yan bindiga ba zai magance rashin tsaro ba

A wani labarin, Babban malamin addinin Islama mazaunin jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi, ya yi ikirarin cewa farmakin da sojoji ke kaiwa kan 'yan bindiga da ke addabar Arewa maso Yamma ba zai magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba.

Malam Gumi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin 6 ga watan Satumba ta shafinsa na Facebook, yayin da yake mayar da martani kan nasarorin da sojoji ke samu a kan 'yan bindiga a dazuzzukan Zamfara.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare

Sanarwar, mai taken: ‘Zamfara: The Flaring of Crisis’, ta jaddada cewa matakin soji kan masu aikata miyagun laifuka “ba mafita bane ko hikima”.

Asali: Legit.ng

Online view pixel