Jihar Kaduna
Wasu mahara sun kai wa mamba mai wakiltan mazabar Jema’a/Sanga a majalisar wakilai, Rt.Hon. Nicholas Garba Sarkin Noma, da wasu mutane da ke cikin motarsa hari.
Dakarun rundunar sojoji sun ragargaji yan bindiga a hanyar Abuja zuwa Kaduna, sun yi nasarar kawar yan ta'addan biyu da jikkata wasu, sun kwato bindigogi biyu.
Kafin rasuwar Sarkin Zazzau, an yi shekara 2 babu sabon Sarkin Adara. Abin mamaki, har yanzu gwamnatin Jihar Kaduna ba ta nada sababbin Sarakuna a yankin ba.
Gwamnatin jihar Kaduna ta soke zaben farko na wanda zai zama sarkin Zazzau, a yanzu haka masu zaben Sarki a masarautar ta Zazzau na kan sabon matakin zabe.
Mawakin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zama dan siyasa, Malam Ibrahim Sale Yala, ya yi murabus daga mukaminsa na mai ba kakakin majalisar Kaduna shawara.
Wata babbar kotu a Kaduna ta yi watsi da bukatar Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta umarci a ci gaba da shari’ar da aka kawo gabanta a kan shugaban na mabiya Shi’a.
Kwanaki takwas kenan da yin jana’izar marigayi tsohon sarkin Zazzau, Dr Shehu Idris, wanda ya yi tsawon shekaru 45 a kan kujerar sarauta, amma babu sabon sarki.
Ana zama da tagumi a birnin Zazzau bayan kwanaki takwas da rasuwar tsohon Sarkin Zazzau, Shehu Idris ba tare da an nada wani sabon sarki da zai gaje shi ba.
An sauya sunayen masu neman sarkin Zazzau, a yanzu harda na hannun daman Gwamna Nasir El- Rufai, Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, cikin wadanda ke neman kujerar.
Jihar Kaduna
Samu kari