Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma

Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma

- Gidajen sarautar masarautar Zazzau da suka hada da na Barebare da Katsinawa sunyi mubaya’a ga sabon Sarki Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli

- Alhaji Munni Ja’afaru, Yariman Zazzau ne ya bayyana hakan a yau Alhamis

- Gidan Katsinawa sun yi wa sarki mubaya’a ne karkashin jagorancin Wamban Zazzau, sai kuma wakilai daga gidajen Barebari, Mallawa da na Malamai

Rahotanni sun nuna cewa gidajen sarautan Barebare da na Katsinawa da ke Masarautar Zazzau sun yi mubaya’a ga sabon Sarki Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli, a yau Alhamis, 8 ga watan Oktoba.

Yariman Zazzau, Alhaji Munnir Ja’afaru ne ya bayyana hakan a yayinda ya ke zantawa da manema labarai bayan gaisuwar da gidajen suka kai wa sarkin a yau Alhamis, jaridar Aminiya ta Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari za ta kafa masana'antun kera takalma da suturu na bilyoyin Naira a Kano da Aba

Gidan Katsinawa sun yi wa sarki mubaya’a ne karkashin jagorancin Wamban Zazzau, Alhaji Abdulkarim Amin, iyalan marigayi Sarki Shehu Idris.

Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma
Gidajen Katsina da Barebari sun kai wa sabon Sarkin Zazzau gaisuwar ban-girma Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

Sauran wadanda suka yi mubaya’ar sun hada da wakilai daga Gidan Barebari, Gidan Mallawa da Gidan Malamai sai kuma wakilan unguwanni.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Daya daga cikin 'yan majalisar masarautar Zazzau ya yi murabus

A gefe guda, mun kawo maku cewa 'yan majalisar nadin sarakunan Zazzau sun amince da zabar Ahmed Bamalli a matsayin sarkin Zazzau, babu dadewa da nada shi.

An nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020. Bayan rasuwar Sarki Shehu Idris da yayi shekaru 45 a karagar mulki.

Jim kadan bayan Sakataran Gwamnatin jihar Kaduna ya isa fadar sarkin Zazzau da sanarwar nadin sabon sarkin, 'yan uwa da abokan arziki da al'ummar Zazzau suka yi ta tururuwar zuwa fada farin ciki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng