Bayan nada shi sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ya shiga fada

Bayan nada shi sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ya shiga fada

- Alhaji Ahmed Bamalli, sabon sarkin Zazzau, ya shiga fadar masarautar

- Sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, na tare da Bamalli a lokacin da ya isa Fadar Sarkin Zazzau

- A yau Laraba, 7 ga watan Oktoba ne Gwamna Nasir El-Rufai ya sanar da nada Bamalli a matsayin sarkin Fulanin Zazzau na 19

Bayan nada shi a matsayin sabon sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli, ya shiga fadar masarautar a yau Laraba, 7 ga watan Oktoba, jaridar Aminiya ta ruwaito.

An tattaro cewa sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Balarabe Abbas Lawal, na tare da Bamalli a lokacin da ya isa Fadar Sarkin Zazzau.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna tawagar sabon sarkin na Zazzau tana isa fadarsa da ke birnin Zaria.

A cikin bidiyon isowar sarkin Fada, an ga mutane da dama suna yi masa rakiya tare da yi masa kirari da san barka.

Ga bidiyon isowar sabon sarkin a kasa:

KU KARANTA KUMA: Allahu Akbar: Sakataren masarautar Kano, Muhammadu Bayero ya rasu

Bayan nada shi sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ya shiga fada
Bayan nada shi sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli ya shiga fada Hoto: @aminiyatrust
Asali: Twitter

Bamalli, wanda kafin nadinsa shi ne Magajin Garin Zazzau a yanzu baya cikin ‘yan takara uku da Masu Zabar Sarki na masarautar suka tura wa Gwamna Nasiru El-Rufai da farko.

Ana ganin kusancinsa da gwamnan ta taka rawa wajen neman a sake lalen sunaye ukun amma Masu Zabar Sarkin suka ce sun yi zaben ne bisa adalci.

KU KARANTA KUMA: Sulaiman Dabo ya ce Gwamnan Kaduna bai kawo kudirin raba Masarauta ba

A yau Laraba ne muka samu sanarwar gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai na sabon Sarkin Zazzau.

Kamar yadda Gwamnan jihar Kaduna ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

Ya gaji marigayi mai martaba, Alhaji Dakta Shehu Idris wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a karagar mulkin.

Kamar yadda takardar ta bayyana, "Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya amince da nadin Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19.

"Ya maye gurbin marigayi Alhaji Dakta Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2020 bayan kwashe shekaru 45 da yayi a kan karagar mulki. "

Alhaji Ahmed Bamalli shine Sarki na farko daga gidan Mallawa a cikin shekaru 100 tun bayan rasuwar kakansa, Sarki Dan Sidi a 1920."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel