Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnatin Bauchi da Kwamishinoni 6 Sun Yi Murabus

Shugaban Ma'aikatan Gidan Gwamnatin Bauchi da Kwamishinoni 6 Sun Yi Murabus

  • Shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin jihar Bauchi, Aminu Hassan Gamawa ya yi murabus domin shiga neman takara a zaben 2027
  • Haka zalika, kwamishinoni shida sun mika takardar ajiye aiki ga Gwamna Bala Mohammed domin bin umarnin kundin dokar zabe
  • Gwamna Bala ya masu fatan alheri a harkokin da suka tasa gaba, tare da nada wadanda za su kula da ma'aikatun da suka bari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi – Shugaban ma’aikata a gidan gwamnatin jihar Bauchi, Hon. Aminu Hassan Gamawa, tare da kwamishinoni shida sun yi murabus daga mukamansu.

Manyan jami'an sun ajiye aikin gwamnatin Bauchi ne domin neman kujerun siyasa daban-daban a babban zaben 2027.

Gwamna Bala.
Gwamna Bala Mohammed yana magana da kwamishinoni a taron Majalisar zartarwa ta jihar Bauchi Hoto: @SenBalaMohammed
Source: Twitter

Sunayen wadanda suka yi murabus

Leadership ta ce daga cikin wadanda suka ajiye mukamansu akwai kwamishinannkusi da harkokin tattalin arziki, Yakubu Adamu, kwamishinan ruwa, Abdurrazaq Nuhu Zaki, da kwamishinar harkokin jin kai, Hajara Yakubu Wanka.

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

Sauran sun hada da kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu,Isa Babayo Tilde, da Faruk Mustapha, kwamishinan ci gaban karkara da ayyuka na musamman, da sauransu.

Gwamna Bala Mohammed ya yi garambawul

Bayan murabus din, Gwamna Bala Mohammed ya amince da sauya wa wasu jami’ai mukamai tare da ba su alhakin kula da ma’aikatun da abin ya shafa har sai an nada sababbin kwamishinoni.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fitar, an umurci Hashimu Yakubu, sakataren gwamna, da ya kula da ofishin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.

Haka kuma, an mayar da kwamishinan ilimi, Dr. Mohammed Lawal Rimin Zayam, a matsayin kwamishinan ma’aikatar wutar lantarki, kimiyya da fasaha, cewar Daily Post.

An ba Antoni Janar kuma kwamishinan shari’a, Hassan Usman El-Yakub, SAN, alhakin kula da ma’aikatar kananan hukumomi da harkokin masarautu, yayin da kwamishinan yada labarai, Usman Usman Shehu, zai kula da ma’aikatar albarkatun ruwa.

Gwamna Bala.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed yana sa hannu a wasu takardun gwamnati Hoto: Sen. Bala Mohammed
Source: Twitter

Haka zalika, Kwamishinan gidaje da muhalli, Danlami Ahmed Kawule, zai kula da ma’aikatar ci gaban karkara da ayyuka na musamman, yayin da Amina Muhammad Katagum za ta kula da ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i.

Kara karanta wannan

Kotu ta amince da bukatar gwamnatin Tinubu a shari'ar mutane 6 da ake zargi da shirin juyin mulki

Kwamishinan kula da harkokin kananan masana’antu, Mohammed Sadiq Shira, zai kula da ma’aikatar kudi, yayin da tsohon DIG Sani Mohammed zai kula da ma’aikatar tsaron cikin gida.

Gwamna Bala ya yi masu fatan alheri

Gwamna Bala Mohammed ya yi wa jami’an da suka ajiye aiki fatan alheri a sabuwar tafiyarsu, tare da bukatar wadanda aka dorawa nauyi su yi aiki tukuru domin tabbatar da dorewar harkokin mulki.

Ya kuma umarce su da su yi aiki tare da manan sakatarori na ma'aikatun domin tabbatar da cewa ayyukan gwamnati na tafiya yadda ya kamata.

Gwamnan Bauchi ya bar PDP zuwa APM

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da komawa APM tare da magoya bayansa.

Majiyoyi suka ce gwamnan ya fice ne tare da magoya bayansa masu biyayya ga bangaren Tanimu Turaki kwanaki biyu bayan hukuncin Kotun Koli.

Kafin ficewarsa daga PDP, Bala Mohammed yana rike da mukamin shugaban kungiyar gwamnonin PDP, wanda ke daya daga cikin manyan mukamai a jam’iyyar adawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262