An shafe tsawon lokaci babu Sarakuna a kasashen Zazzau, Jere da Adara

An shafe tsawon lokaci babu Sarakuna a kasashen Zazzau, Jere da Adara

- Tun 2018 wasu ‘Yan bindiga su ka hallaka Mai martaba Agwom Adara

- Haka zalika Sarkin Jere ya rasu watanni biyar kafin Shehu Idris ya cika

- Har yanzu gwamnatin Jihar Kaduna ba ta nada Magadan Sarakunan ba

Yayin da Zazzagawa su ke jiran su ji an nada sabon Sarki bayan rasuwar Shehu Idris, zai yi kyau a tuna akwai wasu masarautun da ke jiran nadi a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta kawo sunayen wasu sarakunan da su ka rasu kuma har yanzu gwamnatin jihar Kaduna ba ta iya nada wadanda za su gaje kujerunsu ba.

A halin yanzu ba a yankin Zazzau kadai ake jiran gwamnatin Nasir El-Rufai ta nada sabon Sarki ba:

KU KARANTA: Da yiwuwar babban ‘Dan Sarki Shehu Idris, Turaki ya gaji Mahaifinsa

1. Agwom Adara

Tun 2018 wasu ‘yan bindiga su ka kashe Mai martaba Agwom Adara na kasar Kachia, har yanzu babu labarin wanda zai maye gurbin marigayi Dr. Raphael Maiwada Galadima.

Agwom Adara ya na cikin manyan Sarakuna a jihar Kaduna tun sauyin da aka yi a 2010.

2. Sarkin Jere

Watanni shida kenan da rasuwar Sarkin Jere, Dr. Sa’ad Usman, wanda ya yi ta fama da jinya. Har yanzu mutanen yankin Kagarko, ba su da sabon Sarki kamar dai a yankin Zazzau.

An shafe tsawon lokaci babu Sarakuna a kasashen Zazzau, Jere da Adara
Marigayi Shehu Idris Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Wazirin Jere, Alhaji Abdullahi Daniya aka bari ya na gudanar da harkokin fada kafin ayi nadi.

KU KARANTA: Tsohon Sarki Sanusi ya ji dadin cire tallafin man fetur

3. Sarkin Zazzau

A watan jiya ne Alhaji Shehu Idris ya rasu bayan ya shafe shekaru 45 ya na mulkin Zazzau. Kafin ayi wa masarautar Zazzau gutsun-gutsun, Sarkin ta ne ya ke da iko da Jere da Adara.

Sama da mako biyu kenan ana jiran a kammala zaben wanda zai zama magajin Shehu Idris.

Ku na da labari cewa mutane hudu ne su ke kan gaba wajen neman kujerar Sarkin Zazzau. Masu harin gadon sarautar sun hada da Bashir Aminu, Munir Jafar da Aminu Shehu Idris.

Mannir Jafaru ‘dan Sarki Jafaru Isiyaku ne wanda ya fito daga gidan Barebari. Shi kuma Bashir Aminu ‘Da ne wajen Sarki Malam Muhammadu Aminu wanda ya rasu a 1975.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel