Dalilin da ya sa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba, in ji masana tarihi

Dalilin da ya sa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba, in ji masana tarihi

- Masana tarihin masarautar Zazzau su bayyana dalilin da yasa aka samu jinkiri wajen nada sabon sarki

- Sun bayyana cewa hakan ba sabon abu bane a masarautar, domin a cewarsa dama chan nadin sabon sarki kan dauki lokaci

- Shehu Shuaibu ya bayar da misali cewa an dauki lokaci kafin sanar da nada Sarkin Zazzau Jafaru da Sarkin Zazzau Shehu Idris

A yayinda mutane ke ci gaba da nuna ‘kagara kan dadewa da aka yi ba tare da sanar da sabon sarkin masarautar Zazzau ba, masana tarihi sun bayyana hakan a matsayin ba wani sabon abu ba.

Masana tarihin masarautar sun jaddada cewa zaben sabon sarki a daular ya gaji daukar lokaci mai ja.

Kwanaki takwas kenan da aka yi jana’izar marigayi tsohon sarkin Zazzau, Dr Shehu Idris, wanda ya yi tsawon shekaru 45 a kan kujerar sarauta.

Sai dai tun bayan rasuwarsa yan Najeriya musamman mazauna garin Zazzau suke zuba idon ganin wanda zai jagorance su bayan marigayin.

KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe: Kotu ta ci tarar Sanata Abbo N50m saboda cin zarafin wata mace

Dalilin da ya sa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba, in ji masana tarihi
Dalilin da ya sa har yanzu ba a nada sabon sarkin Zazzau ba, in ji masana tarihi Hoto: @dailytrust
Source: Facebook

Kamar yadda shashin Hausa na BBC ta ruwaito, wani masanin tarihi, Shu'aibu Shehu, daraktan cibiyar bincike da ajiye kayyakin tarihi ta Arewa House da ke Kaduna ya ce, jinkirin da aka samu wajen sanar da sabon sarkin Zazzau ba sabon abu bane a masarautar.

Ya ce a duk lokacin da aka yi rashi na sarki a Zazzau, tsarin zaben sabon sarki kan dauki zafi sosai saboda: “kowanne daga cikin gidajen da ke sarauta suna so kujerar ta koma gidansu, kuma cewa ba a cika yin gaggawa ba wajen nada sabon sarki.

“Wannan ba wani abu ba ne sabo domin kasancewar Masarautar Zazzau daya da ta kunshi gidajen masarautu guda hudu da suka cancanta a zabi sarki, ana daukar lokaci domin samo jajirtacce da kwararre, ba sai an yi gaggawar zaben sarki ba," in ji masanin.

Bisa ga tarihi, an dauki lokaci kafin sanar da nada Sarkin Zazzau Jafaru da Sarkin Zazzau Shehu Idris.

KU KARANTA KUMA: Kano ta yi babban rashi: Tsohon babban Alkalin jihar, Shehu Atiku, ya rasu

Shehu ya ce “sai bayan kwana 14 da mutuwar Sarki sannan aka sanar da nada Sarkin Zazzau Jafaru a ranar 15 ga watan Fabrairun 1937.

“Kuma ko lokacin da Sarkin Zazzau Muhammad Aminu ya rasu a Landan ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 1975, ba a nada Shehu Idris ba sai ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar.

“Lokacin da aka zaɓi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris sai da aka jira ƴan majalisar sarki suka zauna suka tantance suka zaɓi waɗanda suka cancanta sannan suka tura wa majalisar sarakuna ta arewa, wacce kuma ta tura wa gwamna wanda kuma ya sanar da wanda aka zaba.”

A gefe guda, mun kawo maku cewa akwai rade-radin da ke yawo a kasar Zazzau cewa gwamnatin jihar tana hararo nada Yariman Zazzau, Munir Jafaru a matsayin sabon sarkin Zazzau, lamarin da yasa aka tsananta tsaro a gidansa da ke Zaria.

Karagar mulkin Zazzau ta zama abun nema tun bayan rasuwar sarkin Zazzau na 18, Alhaji Shehu Idris a ranar 20 ga watan Satumban 2020.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel