Oshiomhole Ya Nemi Tinubu Ya Soke Lasisin MTN da Wasu Kamfanonin Afrika Ta Kudu

Oshiomhole Ya Nemi Tinubu Ya Soke Lasisin MTN da Wasu Kamfanonin Afrika Ta Kudu

  • Sanata Adams Oshiomhole ya yi kira ga Gwamnatin Bola Tinubu da ta soke lasisin kamfanonin Afirka ta Kudu, musamman MTN da DSTV
  • Wannan kiran ya biyo bayan sabon harin ƙyamar baki da ake kai wa ƴan Najeriya a ƙasar Afirka ta Kudu, wanda ya jawo asarar dukiyoyi
  • Sanatan ya jaddada cewa dole ne Najeriya ta mayar da martani mai tsauri domin kare mutuncin ƴan ƙasarta duba da yadda ake cin zarafin su a ƙasar waje

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – Sanatan dake wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana fushinsa a zauren majalisar dattawa game da yadda ake kai wa ƴan Najeriya hari a Afirka ta Kudu.

A yayin zaman majalisar, Oshiomhole ya bayyana cewa lokacin zubar da hawaye da jaje ya ƙare, inda ya buƙaci a ɗauki matakin tattalin arziki mai zafi.

Kara karanta wannan

Pate: Ministan Tinubu ya fadi abin da ya hana shi neman takarar gwamnan Bauchi

Sanata Adams Oshiomhole ya nemi gwamnatin tarayya ta soke lasisin MTN, DSTV
Sanata Adams Oshiomhole a zauren Majalisar dattawa. Hoto: @AdamOshiomhole
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito Adams Oshiomhole ya bayyana wa Majalisar dattawa cewa:

“In ka dake ni, zan dake ka. Ina jin wannan ya dace a tsarin diflomasiyya, domin wannan wata gwagwarmayar tattalin arziki ce.”

Oshiomhole na so a soke lasisin MTN, DSTV

Wannan matsin lamba ya biyo bayan matakin da majalisar wakilai ta ɗauka a ranar Talata na yin Allah wadai da hare-haren, tare da buƙatar gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan diflomasiyya na kare ƴan ƙasa.

Oshiomhole ya ba da shawarar cewa ya kamata Najeriya ta soke lasisin da kamfanin MTN yake da shi na yin aiki a ƙasar nan.

Ya bayyana cewa kamfanin yana samun miliyoyin daloli daga Najeriya a kullum, yayin da ƴan Najeriya ke fuskantar tsangwama a ƙasar Afirka ta Kudu.

Haka kuma, ya yi kira da a soke lasisin kamfanin DSTV, inda ya zargi kamfanin da yin amfani da dabarun da ba su dace ba wajen yin zagon ƙasa ga tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

A gaban Mai Mala Buni: Gwamnan Katsina ya kaddamar da titi mai nisan kilomita 39

Kare 'yan Najeriya dake Afirka ta Kudu

A cewarsa, soke waɗannan lasisin zai buɗe wa kamfanonin gida na Najeriya dama su mamaye waɗannan guraben aikin, in ji rahoton TVC News.

Sanatan ya yi nuni da cewa ƴan Najeriya dake zaune a Afirka ta Kudu ba hutu suka je yi ba, aikin ƙarfi suke yi domin neman na kansu.

Ya bayyana cewa mayar da martani mai ƙarfi ne kawai zai sanya shugaban Afirka ta Kudu ya fahimci cewa ba za a iya tursasa wa ƴan Najeriya ba.

zanga zangar adawa da kyamar baki ta barke a Afrika ta Kudu
Wasu masu zangar zangar kawo karshen nuna kyamar baki a kasar Afrika ta Kudu. Hoto: Ihsaan Haffejee/Anadolu Agency/Getty Images
Source: Getty Images

Kira ga ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU)

A ɓangare guda, Sanata Victor Umeh dake wakiltar Anambra ta Tsakiya, ya nuna damuwarsa kan tsaron ƴan ƙasa, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin fargaba.

Umeh ya yi kira ga ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU) da ta tsoma baki tare da kakaba wa Afirka ta Kudu takunkumi saboda rashin kawo karshen hare-haren da ake kai wa baƙi.

A bangaren Sanata Oshiomhole, ya ƙarƙare da cewa kyamar baki a Afirka ta Kudu tana da alaƙa da siyasar cikin gidan ƙasar, amma dole ne Najeriya ta kare 'yan kasarta.

Kara karanta wannan

Rahoto: Hanyoyi 5 da yakin Iran ya shafi yadda mutane ke samu da kashe kudi a Ingila

Halin da 'yan Najeriya ke ciki a Afrika ta Kudu

Tun da fari, mun ruwaito cewa, 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu, sun yi kira ga gwamnati da ta ɗauki matakai masu ƙarfi domin kare su daga hare-haren ƙyamar baki.

Shugaban ƙungiyar NICASA, Rev. Frank Onyekwelu, ya nuna fargaba kan yadda ake ƙara mayar da ƙyamar baki a matsayin wani abu na yau da kullum a ƙasar.

Onyekwelu ya yi Allah-wadai da yadda wasu ƴan siyasa ke rura wutar ƙiyayya da kuma cin zarafin da wasu jami'an ƴan sanda ke yi wa ƴan Najeriya da sauran baƙi ƴan Afirka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com