Yanzu Yanzu: Gwamna El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna

Yanzu Yanzu: Gwamna El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna

- Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sanar da ranar bude makarantu a jihar

- Yan makarantar kwana za su koma karatu a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba yayinda yan jeka-ka-dawo za su koma a ranar Litinin, 19 ga wata

- Sai dai an gindaya masu sharudan bin matakan kare kai daga annobar korona

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da ranakun Lahadi, 18 da Litinin, 19 ga watan Oktoba, a matsayin ranakun bude makarantu ga daliban makarantun kwana da na jeka-ka-dawo a jihar.

Daliban da zasu koma makaranta sune yan aji shida na makarantar firamare dana aji biyu a karamar sakandire sai kuma yan aji biyu na babbar sakandire.

Babbar mai bayar da shawara ga Gwamna Nasir El-Rufai a kan sadarwa, Maryam Abubakar ce ta wallafa hakan a shafin Facebook.

KU KARANTA KUMA: Kalli budurwar da ta tuka babur daga Lagas zuwa Abuja cikin sa’o’i 13 (hotuna)

Yanzu Yanzu: Gwamna El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna
Yanzu Yanzu: Gwamna El-rufa’i ya sanya ranar buɗe makarantu a Kaduna Hoto: @PulseNigeria247
Asali: Twitter

A bisa ga wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun kwamishinan ilimi, Shehu Usman Muhammad, ya ce:

“Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da ranakun, Lahadi, 18 da Litinin, 19 ga watan Oktoba 2020, a matsayin ranakun komawar daliban makarantun kwana da na jeka-ka-dawo yan SSII da JSSII da daliban aji shida na makarantar firamare a jihar makaranta.

“Saboda haka, ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna na umartan dukkanin shugabannin makarantu da su yi duk wasu shirye-shirye na tarban daliban makarantun kwana a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba yayinda yan makarantar jeka ka dawo kuma a ranar 19 ga Oktoba.

“Ana tsammanin makarantun jami’a za su koma ne bisa lokacin da suka gabatarwa da ma’aikatar. Ana kira ga manyan makarantun da basu gabatarwa da ma’aikatar tsarinsu na bude makaranta ba da su gaggauta aikata hakan.

“Dukkanin shugabannin makarantun gwamnati da masu zaman kansu su lura cewa, dole su bi dukkanin ka’idojin COVID-19 (duba yanayin zafi da sanyin jiki a mashigin makaranta, wajibi ne sanya takunkumin fuska, abun wanke hannu/na kashe kwayoyin cuta da kuma dukkanin tsare-tsaren hukumar NCDC da na kwamitin korona ta jihar).

“Makarantu za su dunga aiki bisa tsarin karba-karba domin basu damar bin ka’idojin COVID-19 yayinda rukunin farko za su yi aiki daga 8:00am zuwa 12:00am yayinda rukuni na biyu za su yi aiki daga karfe 1:00pm zuwa 2:00pm. A aji guda kada a samu fiye da dalibai 20 sannan a bayar da tazara a tsakani.

“Sannan ana shawartan iyaye da su sama wa yaransu takunkumin fuska da sauran kauyayyakin tsafta domin hana yaduwar cutar.

“Ana kuma kira ga shugabannin makarantun gwamnati da masu zaman kansu su yi duk wasu tsare-tsare yadda ya kamata da kuma bin tsarin korona sannan su sanar da kammalar shirinsu na sake bude makarantu.

"Dukkanin makarantu harda na Islamiyya za su tunkari hukumar SQAA domin lamunce masu budewa bayan sun gamsu da duk wani tsari na COVID-19. Tawagar masu saka idanu za su dunga kewayawa domin tabbatar da bin ka’ida.

KU KARANTA KUMA: An kusa wajabtawa wa 'yan Najeriya mallakar lambar NIN - Isa Pantami

“Za a sanar da ranar komawar sauran ajujuwan idan lokaci ya yi. Ma’aikatar na bayar da tabbacin ci gaba da koyar da dalibai ta kafar zamani ta hanyar amfani da Google, rediyo, tashar talbijin da sauransu har zuwa lokacin da komai zai daidata a bangaren ilimi."

A baya mun ji cewa wasu iyaye da dalibai a jihar Kaduna sun yi kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta bi umurnin gwamnatin tarayya na bude makarantu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel