Kasashen Rasha da Ukraine Sun Sanar da Tsagaita Wuta a Yakin da Suke Gwabzawa

Kasashen Rasha da Ukraine Sun Sanar da Tsagaita Wuta a Yakin da Suke Gwabzawa

  • Shugabannin kasashe Rasha da Ukraine sun sanar da tsagaita wuta a yakin da suka shafe shekaru suna gwabzawa ba tare da kawo karshensa ba
  • Sai dai an samu sabani a sanarwar da suka fitar, inda Vladimir Putin da Volodymyr Zelenskiy suka ayyana lokuta daban-daban game da batun
  • A kwanakin baya ma dai kasashen sun sanar da tsagaita wuta domin wani bikin addinin Kirista amma sun zargi juna da warware alkawarin da aka yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Russia - Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa za a tsagaita wuta na kwanaki biyu a yakin da ya ke yi da kasar Ukraine.

Putin ya sanar da cewa za a dakatar da yakin ne a ranakun 8 zuwa 9 ga Mayun 2026 domin bikin nasarar yakin duniya na biyu da Rasha za ta yi.

Kara karanta wannan

Yaki na shirin dawowa: An zargi Iran ta harba makamai masu linzami UAE

Volodymyr Zelenskiy da Vladimir Putin
Vladimir Putin a hagu yana waya da Volodymyr Zelenskiy a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Reuters ta rahoto cewa Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy ya mayar da martani da nasa shirin tsagaita wuta da zai fara tun daga daren 5 zuwa 6 ga Mayun 2026.

Batun tsagaita wutar Rasha/Ukraine

Putin ya fara ambaton yiwuwar tsagaita wutar ne a makon da ya gabata yayin wata tattaunawa ta waya da Shugaban Amurka Donald Trump, inda aka danganta hakan da bikin cika shekaru 81 na nasarar yakin duniya na biyu.

Sai dai Ukraine ta nuna shakku kan tsagaita wuta na dan lokaci maimakon daukar matakin kawo karshen yakin gaba daya.

Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar cewa tsagaita wutar na kwanaki biyu zai gudana a ranakun 8 da 9 ga Mayun 2026, tare da fatan Ukraine za ta bi sahu.

Ta ce sojojin Rasha za su dauki duk matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron bukukuwan tunawa da shan kashin Jamus a yakin.

Kara karanta wannan

Lamari zai dagule: Iran ta ja kunnen Trump game da tura sojoji Hormuz

Rasha ta gargadi kasar Ukraine

Sight Magazine ta wallafa cewa Rasha ta gargadi cewa duk wani yunkuri daga Ukraine na kawo cikas ga bukukuwan zai fuskanci martani mai tsanani.

“Idan gwamnatin Kyiv ta yi yunkurin aiwatar da shirinta na kawo cikas ga bikin cika shekaru 81 na nasarar yakin, rundunar sojin Rasha za ta kai harin makamai masu linzami mai karfi tsakiyar Kyiv,”

In ji sanarwar.

Ta kara da cewa Rasha na da karfin kai irin wannan hari tun da dadewa amma ta guji yin hakan saboda dalilan jin kai:

“Haka kuma muna gargadin fararen hula a Kyiv da ma’aikatan jakadanci na kasashen waje da su bar birnin cikin gaggawa,”
Wani giri da aka kai wa hari a Ukraine
Ginin da Rasha ta kai wa hari a Ukraine a ranar 1 ga Mayu, 2026. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Martanin Shugaban Ukraine ga Rasha

Zelenskiy kuwa, a wani rubutu da ya fitar bayan halartar taron Kungiyar Siyasar Turai a Armenia, ya ce Ukraine za ta aiwatar da nata tsagaita wuta tun daga tsakar dare na ranar 5 ga Mayun 2026.

Ya ce Rasha ta gaza amsa kiran Ukraine na tsagaita wuta na dindindin, yana mai cewa matakin da Ukraine ta dauka ya dogara ne da darajar rayuwar dan Adam.

Kara karanta wannan

Shirin dawowa yaki: Kasar Iran za ta kai dogayen hare hare kan Amurka

“Rayuwar dan Adam ta fi kowace irin bikin cika shekara muhimmanci,”

in ji shi.

Tsagaita wutar da suka yi a baya

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Vladimir Putin ya sanar da tsagaita wuta tsakanin shi da Ukraine domin bikin Easter a kwanakin baya.

Putin bukaci sojojin Rasha su kiyaye tsagaita wutar daga karfe 4:00 na yammacin ranar da yarjejeniyar ta fara aiki har zuwa wa'adin da aka sanya.

Yayiin da ya yi fatan Ukraine za ta cika alkawari, Putin ya ce sojojinsa su kasancewa cikin shiri don dakile shirin kai farmaki daga waje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng