Kwanaki 8 babu sabon sarki: Ana zaman jiran tsammani a garin Zazzau

Kwanaki 8 babu sabon sarki: Ana zaman jiran tsammani a garin Zazzau

- Ana zaman jiran tsammani a birnin Zaria bayan kwanaki takwas da rasuwar tsohon Sarkin Zazzau, Shehu Idris ba tare da an nada sabon sarki ba

- Majiyoyi dai na zargin hakan ta kasance ne saboda sako siyasa da aka yi a cikin lamarin

- A yanzu dai wuka da nama na a hannun Gwamna Nasir El-Rufai

Ana zaman fargaba a birnin Zaria bayan kwanaki takwas da rasuwar tsohon Sarkin Zazzau, Shehu Idris ba tare da an nada wanda zai gaje shi ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa ba don siyasa da ya shigo lamarin ba, da an nada sabon sarki jim kadan bayan addu’an bakwan marigayi sarkin, wanda aka gudanar a jiya Lahadi.

Bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya nuna cewa akwai rashin kwanciyar hankali a birnin tun ranar Juma’a, lokacin da labari ya bayyana cewa masu nada sarki sun mika sunayen mutane uku ga Gwamna Nasir El-Rufai.

Babban batu da mazauna yankin ke ta tattaunawa a ranar Lahadi shine kan wanda zai zama sabon sarki.

Kwanaki 8 babu sabon sarki: Ana zaman jiran tsammani a garin Zazzau
Kwanaki 8 babu sabon sarki: Ana zaman jiran tsammani a garin Zazzau Hoto:@dailytrust
Source: Facebook

Mutanen da ke goyon bayan yarimomin na ta tattauna da mammakin da wadanda suke so ke dashi.

KU KARANTA KUMA: Babu gaskiya a ‘bidiyoyin’ nada Yariman Zazzau kan sarauta inji San Turaki

An samu yawan mutane a gidan Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru, wanda ya kasance daya daga cikin yan takarar na GRA.

An gano mutanen suna ta tattauna batutuwa kan dan takarar da suka fi so, wannan ne ma dalilin da yasa suka taru a mashigin gidansa.

An kuma gano mutane a Sabon Gari, gidan Alhaji Bashar Aminu na Zariya, inda a nan ne yayi yawancin rayuwarsa a lokacin da yake aiki a matsayin hakimin yankin.

Haka zalika an gano abokai da masu fatan alkhairi na Alhaji Aminu Shehu Idris, a fadar Zazzau suna fatan ganin ya zamo sabon sarki.

KU KARANTA KUMA: Yanzu yanzu: Mayaƙan Boko Haram sun sake kaiwa tawagar Gwamna Zulum hari ranar Lahadi

Sannan kuma, yan daular Mallawa da suka cika da mamakin rashin ganin sunan Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, wanda ke rike da sarautar Magajin Garin Zazzau, yanzu suna da tsammanin yin nasara bayan dawo da sunansa a masu takara.

A cewar wata majiya, cire sunan Ahmad Bamalli daga jerin wadanda masu zabar sarkin suka mika wa gwamnatin tun da farko bai yi wa gwamnan dadi ba.

Hakan ne ya sanya aka kara mayar da sunansa domin a ba gidan sarautar da ya fito na Mallawa damar fafatawa da su.

A cewar majiyar, “Bayan sauya jerin sunayen, yanzu haka sunan Bamalli ne ma a sama.

“Gwamnan na fuskantar matsin lamba kan ya ba gidan Mallawa sarautar ne saboda rabonsu da hawanta an haura shekaru 100.

“Ko shakka babu yanzu lamarin baki daya siyasa ta shiga ciki, akwai masu neman biyan bukata da yawa.

“Ko da yake gwaman na kokarin zama a tsakiya, amma babu tabbas zai iya yin hakan a wannan lokacin, musamman kasancewar shima yana da tasa bukatar,” inji majiyar.

Sannan, wata majiyar a fadar gwamnatin Kaduna ta ce gwamnatin ba ta ji dadin sunayen farkon ba sakamakon Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ne ya samu maki mafi yawa.

Suna kuma zargin yana samun goyon baya daga wani jigo a jam’iyyar adawa ta PDP a jihar.

Majiyoyi a Kaduna sun bayyana cewa duba da abubuwan da suka faru a daren ranar Lahadi, yanzu El-Rufai ne kadai ya san wanda zai zama Sarkin Zazzau na gaba.

“Gwamnan ya gana da masu ruwa da tsaki da dama kuma yana duba abubuwa da dama, ciki har da kalubalen da zai iya biyo baya in ya yi fatali da shawarar masu zabar sarkin,” in ji majiyar.

“Yanzu shawara ta rage ga gwamnan ya zabi wanda ya ke so,” inji majiyar.

Da aka tuntubi mai ba gwamna El-Rufai shawara a kan labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, bai amsa kiran waya ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel